A cigaba da shirin Big Brother da ke gudana a yanzu haka, masu fafatawa da dama sun nutse cikin kogin soyayya da juna, wasu kuma suna ta sake saken kitsa yadda za su ratsa tsakanin abokan takarar su su yi zarra a gasar.
Soyayyar da yayi fice a gidan Big Brother shine na Khalid da Daniella, soyayyar da ko wa ke gani babu kamar sa a wannan gida baya ga na Sheggz da Bella.
Khalid ɗan asalin garin Jos ya tsindima cikin soyayya da Daniella gadan-gadan wanda da yawa cikin masu bibiyan wannan shiri suna cewa soyayyar ta su ta yi karfin gaske wanda ake ganin zai iya zarce gidan Big Brother idan dai suka ci gaba a haka.
Ita ko Sarauniyar kyaun Najeriya, Beauty Takura ta kwafsa na a gidan Big Brother, in da ta kafa tarihin da ba a taba kafawa ba.
Beauty ce wacce aka kora a gidan Big Brother kwanki 14 kacal daga dara shirin.
A baya an kori wasu amma na ta korar ya yi wuri fiwlye da na sauran.
A wannan makon an sallami mutane biyu cikin ƴanwasa 5 da aka zaɓa su ne za a iya sallama daga gidan. Waɗanda aka sallama sun haɗa da Cyph da ChrityO, wanda makin su bai kai yawan na sauran mutum ukun da aka ambata sunan su za aiya sallanar su daga gidan Big Brother ba.
Wasu da dama musamman iyaye da suka tattauna da wakiliyar PREMIUM TIMES HAUSA, Aisha Yusuf, sun bayyana rashin gamsuwar su ga wannan shiri.
Da yawa sun ce shirin ya ci karu da irin al’adun mu da tarbiyyar da aka ta so da shi.
Sai dai kuma kamar yadda ake saka a wau shirin da finafinan da ake kallo, suna gargaɗin kada iyaye su bari yaran da basu wuce shekaru 18 ba su rika kallo.
” Na san abu ne ake yi don nishaɗi kuma gasa ne, amma kuma ni gargaɗi na shine kada iyaye su ruka bari yara na kallo domin shiri ne na manya waɗanda suka mallaki hankalinsu. Shima dai kamar fim din soyayya ne na turawa da ake kallo.”
Discussion about this post