Dibi da yawaitar matsalolin fitsara tsakanin dalibai maza da dalibai mata da muke fama da su na tsawon shekaru, Ma’aikatar Ilimi ta Jahar Bauchi, idan ta samu sahhalewar Gomnati, tana so ta fadada tsarin MATA ZALLA a makarantun “sakandaren wuni” (ko je-ka-ka-dawo, ko Day Secondary Schools a Turance), duk inda ake da ikon yin haka din. Wannan a fahimtarmu ya zama wajibi.
Tarihi
Raba daliban sakandare mata daga ƴan uwansu maza a Jahar Bauchi ya samu asali ne tun lokacin marigayi, maigirma, Gomna Tatari Ali, lokacin da makarantun kwana (Boarding secondary schools) kadai ake da su wanda a cikinsu akwai wandanda maza da mata ke gwamutse (co-education). Ko da aka yi ta kirkiro makarantun wuni daga baya, ba a rarrabe tsakanin na mata da maza ba saboda akasarinsu a matakin kananan sakandare suke, watau Junior Secondary Schools (ko “juniya” a takaice). Ci gaba kawai aka yi da tsarin firamare inda yara maza da mata ke cakude a cikin azuzuwansu. Daga wadannan makarantun juniya, sai yaro ya tafi makarantar babbar sakandare ta kwana a wancan lokacin.
Da ilimi ya bunkasa aka fara bude makarantun jeka-ka-dawo na babbar sakandaren wuni a garuruwan da ake da kananan sakandare, bayan zamanin Shagari, ba a dabbaka wancan tsari na mata-zalla wanda aka yi wa makarantun kwana a zamanin Tatari Ali ba, saboda karancin makarantun da kuma ganin cewa ai ba kwana daliban suke yi a makarantun ba, wuni kawai suke yi.
Yanzu muna ganin lokaci ya yi da tsarin zai hada da makarantun wuni, kuma da dalilanmu.
Dalilai
Akwai dalilai 6 kwarara na tsarin “mata-zalla” a makarantun wuni.
1. Bayan shekaru 35 abubuwa da yawa sun faru kuma tarbiyyar al’umma ta tabarbare musamman bayan wanzuwar manyan wayoyi inda kananan dalibai, sabon balaga, (adolescents), ke hawa dandalin sada zumunta suna koyon fitsara kala-kala. A shekarun baya an yi fama da matsalar auratayya tsaknain daliban aji guda, wacce har yanzu tana nan, a wani kes din har da daukan ciki.
Wannan tsarin “mata-zalla” ya kara karfafa ne da muka ga abinda ya faru a “Markers Day” na bana inda a ranar gama rubuta jarrabawar NECO dalibai suke rubutu a kan yunifom din junansu, da chashewa, da daukan hotuna masu ta da hankali suna yadawa a yanar gizo. Hoton da ya fi tayar wa kowa hankali shi ne wanda wata yarinya ta kwaye hijab dinta a filin Allah-taala, tana sheke dariya, wani yaro ya rika rubutu a kan nononta. Kuma ba ita kadai ba ce ta yi haka a wannan makarantar. Duk fitsarar uba, idan ya ga wannan hoto, dole hankalinsa ya tashi. Zan so da a ce na sa hoton a nan don ya zama hujja, amma gaskiya ba zan iya ba, duk da matsayina na rikakken dan’boko.
2. ‘Ya’yan talakawa mata a makarantun wuni su suka fi zama “victims” na wannan fitsarar saboda ba su da wadatar da za ta kange su daga sharrin maza. A kes din da na ambata batun daukan ciki da wata daliba ta yi a sama, wanda daya ne kawai a cikin guda uku da aka gano a wata makaranta a wannan shekarar, sadakin da yan’mazan suka biya wa dayansu shi ne na doguwar riga da ake yayi, wata kuma wayar hannu, ta karshe ita kuma takalman sawa. In banda talauci da ya mamaye al’umma, me zai jawo wannan? To amma iyaye talakawa ba yanda suka iya, an fi karfinsu, a dole suke hakura. A nan, kare muradinsu ya zama dole wajen hukuma idan da hali.
3. Shekarun murahaka, watau shekarun balaga, shekaru ne da jikin yara ke shiga canje-canje ta nahiyoyin dabam-dabam. Wadannan canje-canje, su ke sa yara su yi wasu abubuwan cikin wauta wacce take cutar da su a rayuwa har abada. Idan sun je jami’a, sun kara shekaru, sai ka ga hankali ya zo musu, sun nutsu, suna yin abu sese-sese. Don haka kare su a wannan matakin balaga, a shekarun makarantun sakandaren juniya zuwa siniya, musamman daga shekarun 14 zuwa 18, ya zama dole. Idan da hali aka hada da kannensu na juniya masu shekaru 12 zuwa 14, shi ma zai taimaka.
4. In mun lura, tun karatun litattafan farko, Musulunci ya tsara raba yara da zaran sun kai shekara 10, tun kafin su balaga, wajen kwanciya a gidajen iyayensu. Zancen baligai su cakuda a makaranta, maza da mata, bai taso ba a wancan zamanin. A namu zamanin, cikin tsarin ilimin zamani, ana yi ne bisa lalura. Amma da zarar akwai halin da za a raba su, ko da kuwa a matakin jam’i’a ne, ya wajaba a raba su. A ka’idar usulu, malamai sun ce mana idan lalura ta kau, sai a tabbatar da haramci. Idan da nama mai kyau, mushen da ake ci sai ya haramta.
5. Akwai garuruwa da iyalai da ke hana ‘ya’yansu mata wucewa siniya sakandare don ba sa don cakwuda da maza. Na samu wannan halin a wata helkwata ta karamar hukuma. Tsarin mata zalla zai janye wannan fargaba ya ba yaran damar kammala karatunsu na sakandare.
6. A karshe, tsarin mata-zalla zai ba da damar koya wa mata dabi’un da suka dace da rayuwarsu. Akwai abubuwa da yawa da ya kamata mace ta sani game da jikinta da rayuwarta a shekarun balaga don inganta rayuwarta na zamantakewa, da tattalin arziki da lafiyarta, da tsareta daga sharrin namiji, wadanda ba zai yu a tattauna su tana cakude da maza ba. Masu kungiyar Centre for Girl Child Education, wacce ta yan’uwanmu mata ne yanboko, Su Dr. Mardiyya Siraj, da suka gwada ba da irin wadannan darussa a Jahar Bauchi na shekaru hudu sun yi murna sosai da jin za a samar da makarantu zalla tunda zai warware duk matsalolin da za a samu na wanzar da irin wannan ilimin ga yanmatan a yanzu da yake kungiyar ta gama aikinta a Jahar. Kawai za mu mai da shi darasi ne cikakke, mai zaman kansa na shekara daya, kamar sauran darussa da za a koyar a irin wadannan makarantun na tuwona-maina.
Tsari
Tsarin a Bauchi zai zo da sauki saboda za a yi shi ne a garuruwa da unguwanni da ake da tagwayen makarantu. Sai kawai a mai da makaranta guda ta maza, guda ta mata.
Misali, makarantun Kofar Idi da Kofar Wambai, sai a mai da makarantar Kofar Idi ta mata-zalla, Kofar Wambai ta maza. Haka, Games Village da Federal Lowcost, sai waccar ta zama ta mata-zalla, wannan ta maza. Makarantar Sa’adu Zungur karib dinta, mai azuzuwa 78, sai a bar wa mata-zalla ita, su kuwa yan mazan da ke cikinta a mai da su makwabtan makarantu biyu na Bakari Dukku—Comprehensive da Day. Dss.
Wannan makarantar wuni ta Saadu Zungur, ta kai ta hadiye duk yanmatan da ke cikinta, da na Bakari Dukku guda biyun, da na Dr. Ibrahim Tahir, da na Army Barrack, da kuma wadanda za a dauka sabbi daga unguwannin Kobi, da Jahun, da Baba Sidi da sauran unguwanni na kusa. Tunda za a rika gudanar da ita safe-da-yamma, za a samu azuzuwa 156 ke nan.
Idan an kare, a garin Bauchi, da Azare, da Misau, da Ningi, da Jama’are, da Dass, da Tafawa Balewa da Tilden Fulani, kaf, ba inda dalibai mata za su cudanya da mata a matakin siniya. Kuma za a yi haka cikin ruwan sanyi, ba tare da an kashe sisin kobo ba tunda makarantun da malaman maza da mata suna nan isassu a cikinsu.
A fitowa da tsarin mata-zalla, mun yi la’akari da nisan takawa da daliban za su yi daga gidajensu da samuwar makarantu biyu ko uku a kusa da su. A inda babu damar rabawa, al’umma sai ta hakura sai dama ta samu.
Malamai
Za mu yi kokari mu tabbatar da cewa malami namiji idan ba kan lalura ba ba zai koyar a makarantar mata-zalla ba, kuma bayan cikakken tantancewa. Duk an yi tunanin wannan.
Tuntuba
Mun rubuta memo wa Maigirma Gomna wannan shawarin na Mata-Zalla, ya ce zai amince da shi idan an tuntubi jama’a kuma suka nuna amincewarsu da haka. Wannan shi ne makasudin kawo zancen nan. Hakaza, za mu tattauna ta, kamar yanda Gomna ya ba da shawara, a kafofin rediyo da talabijin a manyan garuruwan Jahar Bauchi a wanna satin kafin mu koma gunsa don neman sahhalewar Gomnatinsa.
Da ma a nan Ma’aikatar Ilimi, a cikin gida, mun gabatar da shawarar Mata-Zalla din a gaban Komiti na Darektoci, da Principals na makarantun, da hukumar SUBEB wacce muke son ita ma ta dabbaka tsarin a makarantunta inda ake da damar yin haka. Kowa ya yi maraba da tsarin. Saura jama’ar gari, malaman addinai, da SBMCs/PTA.
Kira
Muna kira ga jama’a da su bayyana ra’ayinsu game da wannan tsari na Mata-Zalla. Idan akwai masu ra’ayin a cigaba da tsarin yanzu duk da matsalolin tarbiyya da yake bayarwa sai su fada tare da dalilansu. Za mu saurari kowa.
Allah ya shirye mu zuwa ga sama wa al’ummarmu maslaha ga abinda ya dame ta, da bin ka’idonjinsa wajen yin haka mastada’a.
Na gode.
Dr. Aliyu U. Tilde
Kwamishinan Ilimi na Jahar Bauchi
Discussion about this post