Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya musanta wasu rahotannin da aka buga, waɗanda aka ce ya ce idan ya zama shugaban ƙasa zai cicciɓi jami’o’in gwamnatin tarayya ya damƙa su a hannun jihohi.
Kakakin Yaɗa Labaran Atiku mai suna Paul Ibe ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Ibe ya ce sun fahimci ana yaɗa wasu rahotanni da nufin tozarta Atiku ta hanyar canja masa maganar da ya yi dangane da jami’o’in gwamnatin tarayya, a wurin Taron Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya na 62 da ya gudana a Legas.
“Rahoton da aka ce Atiku zai maida jami’o’in gwamnatin tarayya a hannun jihohi idan ya ci zaɓen 2023, ba gaskiya ba ne, sharri ne kuma bai yi daidai da abin da Atiku ya faɗa a wurin taron ba.
“An yi masa tambaya ne a kan batun tsitstsinka ikon gwamnatin tarayya, wanda kuma ya na daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin sa za ta yi idan ya ci zaɓe.
“Abin da ɗan takarar na PDP ya furta cewa ya yi za a daddatsa wasu ayyuka na gwamnatin tarayya amma bai ce zai maida jami’o’in gwamnatin tarayya a hannun jihohi ba.
“Saboda rahoton da wasu jaridu su ka buga ba gaskiya ba ce, sun karkatar da masu karatu daga gaskiyar abin da Atiku ya furta a wurin taron.” Inji Ibe.
Ya ce da aka tambayi Atiku waccan tambayar, ya amsa da fara bada labarin abin da ya faru tsakanin sa da wani farfesa.
“Atiku ya ce Amurka na da kamanceceniyar tsarin ilmi da irin jami’o’in Najeriya na farkon lokacin samun ‘yanci, inda jami’o’in a lokacin su na ƙarƙashin gwamnatocin lardi-lardi ne.
Ya ce daga nan sai Atiku ya ce idan aka yi kyakkyawan tsari, to waɗannan jami’o’i za su iya zama ƙarƙashin lardi-lardi amma na gwamnatin tarayya.
“Atiku ya ce ilmi zai kasance abin da zai zama sahun farko na ayyukan gwamnatin tarayya idan ya zama shugaban ƙasa.”
Daga nan ya ce a yi watsi da wancan rahoton ƙarya da aka riƙa watsawa kan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
“Atiku na nan kan bakan sa na alƙawarin da ya yi cewa idan aka zaɓe shi, zai gyara dangantakar gwamnati da ƙungiyar ASUU da kuma ɗalibai.
Discussion about this post