A karon farko tun bayan ziyarar da ɗan takarar shugaban ƙasa a APC, Bola Tinubu ya kai wa Olusegun Obasanjo a gidan sa da ke gonar sa ta Otta, a Jihar Ogun, tsohon Shugaban Ƙasa Obasanjo ya fito ya yi maganar kore wasu maganganu da ya ce su na yawo a kafafen sadarwa.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Obasanjo, Kehinde Akinyemi ya fitar a ranar Asabar, Obasanjo ya musanta cewa ya na goyon bayan takarar Tinubu a zaɓen 2023.
Ya ce maganganun da su ka keɓe su ka tattauna batun ne na ‘yan uwantaka ba na siyasa ba.
Ya ce, “masu yaɗa cewa wai na goyi bayan takarar Tinubu, makusantan ɗan takarar ne kawai, kuma hakan da su ke yi masa cutar sa su ke yi, ba taimakon sa ba.”
Cikin sanarwar dai Akinyemi ya ce Obasanjo bai amsa yardar buƙatar da Tinubu ya yi masa ba.
“Ni ban ce ba na goyon bayan takarar sa ba, kuma ban ce masa ina goyon bayan takarar sa ba.” Cewar Obasanjo.
A ziyarar da Tinubu ya kai masa, sun shafe sa’o’i uku su na ganawa, amma kuma bayan fitowar sa, Obasanjo bai gana da manema labarai ba.
Cikin tawagar ‘yan rakiyar Tinubu akwai Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, tsoffin gwamnoni irin su Segun Osoba, Gbenga Daniel, Bisi Akande da tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu.
Discussion about this post