Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya nesanta kan sa daga rahotannin da su ka ce ya maka Atiku Abubakar da Gwamna Aminu Tambuwal kotu kan sakamakon zaɓen fidda gwanin PDP.
Ya ce idan ma wani ya kai ƙarar, to ba da sanin sa ba, kuma ba da umarnin sa ba.
Wike ya ce kawai sharrin makusantan Atiku ne su su ka kitsa wannan tuggun.
Ya ce tun bayan da aka kammala zaɓen da ya yi niyyar garzayawa kotu, ta tuni aikin gama ya gama.
“Amma ban je kotu kafin cikar wa’adin kwanaki 14 bayan zaɓe da dokar ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta tanadar ba, me kuma zan je na yi yi yanzu?
“Lokacin da na taya Atiku murna sai da na faɗa masa cewa makusantan ka ne babbar matsalar ka. Kuma su ne za su taɗiye maka ƙafa ka kasa cin zaɓen 2023.
Da ya ke magana a Fatakwal yayin buɗe wasu ayyukan inganta rayuwa a ranar Juma’a, Wike ya ce ya na jiye wa Atiku matsalar makusantan sa, waɗanda Wike ɗin ya ce idan ba kakkaɓe ɓatagarin su ya yi ba, to ba zai taɓa yin nasara ba.
Wannan ne karo na huɗu da Atiku ya taɓa fitowa takarar shugabancin Najeriya.
Discussion about this post