Ambaliya sanadiyar ruwan sama mai karfi ya share kadar Barsika dake a karamar hukumar Gwaram ta Jihar Jigawa.
Gadar mai mahimmaci yana hada garuruwan Kano da jahohin Gombe, Taraba da Adamawa.
A bara a watan agusta, karyewar gadar tayi sanadiyar mutuwar mutum 21 cikin har da wasu wadanda suka dawo daga neman aikin soja, akan hanyarsu ta kumawa gida.
Mazauna yankin sunyi Allah wadai da irin aikin da akayiwa gadar a bara lokacin da ya karye. Titin mallakin Jihar Jigawa ne.
Yan Sanda a Jihar ta Jigawa a yau Lahadi sun shawarci matafiya da canja hanya mafi dacewa saboda ahalin yanzu babu hanya, sanadiyar karyewar gadar, cewar kakakin Yan Sanda, Lawan Adam.
Lawan Adam yace gadar ya karye ne a daidai kauyen Rabadi dake kan hanyar Basirka zuwa Gwaram sanadiyar ruwan sama mai karfi da akayi a daren jiya.
Shi ma shugaban gamayyan kungiyoyin farar hula na Jigawa, Musbahu Basirka, yayi kiraga Gwamnatin Jiha, da ta gaugata gyara gadar saboda mahimmacinta a yankin.
Musbahu Basirka, wanda dan asalin yankin ne yace karyawar gadar tana barazana ga rayuwa da tattalin arzikin mazauna yankin mai tarin Al’umma, yace ta hanyar ne ake shige da ficen kayan masarufi na yau da kullum.
Discussion about this post