Shugaban ma’aikatan gwamnati na jihar Filato HoS Sunday Hyat ya bayyana cewa albashin wata biyu ne kacal ma’aikatan jihar ke bin gwamnati ba wata shida ba.
Hyat wanda ya fadi haka ranar Asabar din da ya gabata a garin Jos ya ce ya fadi haka ne baya labarin da ya kareda kafafen labarai cewa gwamnatin jihar Filato na cikin jerin jihohin kasar da basu biya albashin ma’aikatan su na tsawon watanni 6.
“Domin guje wa duk wani shakka Ina mai tabbatar muku cewa albashin wata biyu ne kacal gwamnati bata biya ba.
Ya ce gwamnan jihar Simon Lalong na kokari wajen ganin ya biya duk albashin ma’aikatan gwamnati a jihar.
“Kowa na da masaniya game da yadda gwamnatin Lalong ke kokari wajen biyan albashin ma’aikata a shekarun baya.
” Gwamnati ta ƙasa biyan albashin wata biyu saboda matsalar karancin kudaden shiga.
“Amma Ina mai tabbatar muku da cewa gwamnati za ta yi kokari wajen ganin ta biya albashin ma’aikatanta kafin watan Nuwamba.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin rahoton kungiyar BudgIT ta fitar da rahoton inda ta ce aƙalla jihohi 12 a cikin jihohin Najeriya 36 ba su biya aƙalla albashin wata ɗaya ko sama da haka ba ya zuwa 28 Ga Yuli, 2022.
Daga cikin jihohin akwai jihar Taraba, Edo, Ebonyi, Ondo, Filato, Imo, da Abiya. Rahoton ya ce sun ƙi biyan ma’aikata albashin kuma sun kasa biyan ‘yan fansho haƙƙoƙin su.
Jihar Abiya ba ta biya wasu daga cikin ma’aikatan jihar albashi ba tsawon watanni 22.
Jihar Abiya ta kasa biyan albashin ma’aikatan manyan makarantun gaba da sakandare tsawon watanni shida, yayin da Jihar Ebonyi ba ta biya haƙƙin ‘yan fansho na tsawon watanni shida ba.
Discussion about this post