1. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ya yi sabbin jarista ga mutane 12, 298, 944. Kafin nan akwai masu rajista har mutane 84, 000, 484. Wato a yanzu akwai waɗanda su ka yi rajista har 96, 299, 428 kenan.
2. Matasa miliyan 8.7 ne masu shekaru daga 18 zuwa 34 aka yi wa rajista kwanan nan. Masu shekaru 35 zuwa 49 kuwa an samu miliyan 2.4. Sai kuma mutum 856, 017 masu shekaru daga 50 zuwa 69. Masu shekaru 70 zuwa sama kuwa an samu mutum 127, 541.
3. Matan da aka yi wa rajista sun kai 6, 224, 866. Maza kuma 6, 074, 078.
4. Jihohi uku da ke kan gaba wajen yawan waɗanda su ka rajista kwanan nan, sun haɗa da: Legas mutum 585,629. Sai Kano mai 569, 103. Ta uku Delta mai 523, 517.
5. Jihohi masu ƙarancin waɗanda su ka yi rajista kwanan nan, su ne: Ekiti mutum 124, 844. Mai bi mata Jihar Yobe mai 152, 414. Sai Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja mai 211, 341.
6. Mutum miliyan 12 ɗin da INEC ta ce an ƙara samu sun yi rajista, sun gaza ga miliyan 20 zuwa miliyan 36 da INEC ta ci burin tunanin samu tun da farkon fara ƙarin yin rajistar. Saboda INEC ta sa ran samun aƙalla masu rajista har miliyan 120 kafin zaɓen 2023.
7. Wannan adadin waɗanda su ka yi rajista zai ragu idan INEC ta yi tankaɗe da rairayar waɗanda su ka yi rajista sau biyu ko sama da sau biyu, sai kuma waɗanda su ka yi rajista ba daidai ba.
8. Waɗanda su ka yi rajista daga Janairu zuwa Yuni za su samu katin su cikin Oktoba.
9. Waɗanda su ka yi rajista daga 1 Ga Yuli zuwa 31 Ga Yuli, za su karɓi katin su cikin Nuwamba.
10. Yankin Arewa maso Yamma, wanda ya ƙunshi jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Kaduna, Zamfara, Sokoto da Kebbi ne mafi yawan masu rajista har miliyan 22.67.
11. Yankin Kudu maso Yamma, mai jihohin Ekiti, Ondo, Oyo, Ogun, Osun da Legas ne na biyu da masu rajista miliyan 18.3.
12. Kudu maso Kudu mai jihohin Delta, Bayelsa, Edo, Ribas, Cross River da Akwa Ibom ne na uku da rajista miliyan 15.2.
14. Na haɗu a yawan masu rajista shi ne Yankin Arewa ta Tsakiya mai miliyan 14.1. Su ne jihohin Neja, Filato, Nasarawa, Benuwai da FCT.
15. Arewa maso Gabas mai jihohin Adanawa, Barno, Bauchi, Gombe, Yobe da Taraba ne na biyar masu rajaista miliyan 12.8.
16. Kudu maso Gabas da ya haɗa Abiya, Enugu, Imo, Ebonyi da Anambra ne na shida mai rajista miliyan 11.49.
Discussion about this post