Ɗan Takararar Majalisar Wakilai ta Tarayya na mazabar Kazaure, Roni, Yankwashi da Gwiwa, a karkashin Jam’iyyar APC, Muhammad Mukhtar, yace idan Allah ya bashi nasara a zabe mai zuwa zai banbanta da Dan Majalisa mai ci, Muhammed Gudaje Kazaure ta hanyar gabatar da kudirori masu ma’ana domin cigaban talakawa da al’ummar yankinsa gaba ɗaya.
Mukhtar ya shaidawa PREMIUM TIMES HAUSA a hira da yayi cewa so da kauna da al’ummar yankin suke masa da kuma neman wakili nagari yasa ya kayar da da Gudaje Kazaure da wasu ƴan takarar kujerar ta majalisar wakilai ta tarayya.
Mukhtar wanda shi ne shugaban Karamar Hukumar Kazaure mai ci ya samu nasara ne a zaben fidda gwani na Jam’iyyar APC da aka yi a watan Mayu.
Mukhtar ya sami kuri’u 89, Muhammad Zakari, ya sami kuri’u 70, sai kuma Muhammad Gudaje ya samu kuri’u 26.
Amma bayan zaben na cikin gida, Gudaje Kazaure yayi zargin cewa Gwamna Muhammad Badaru wanda suka ɗaɗe suna takon tsaka shi ne ya yi maƙarkashiyar doka shi da kasa a zaɓen fidda gwanin.
Mukhtar ya ƙara da cewa mutane yanzu sun waye, wanda zai taimaka musu ya kawo musu cigaba hqr inda suke shine suke bi, kuma dalilin haka ne ya sa gaba ɗaya suka bi tafiya ta.
” Idan aka zabe ni zan kawo wa al’ummar shiyya ta wato Kazaure, Yankwashi, Roni da Gwiwa abinda Gudaje bai kawo musu na cigaba ba.
” Zamu taimakawa mutanen mu saboda muna da kusanci da dasu wanda shi ne bambamci na da Gudaje. A yanzu ni ne shugaban karamar Hukuma, Mutane suna ganin kulawa da ake nuna musu a koda yaushe, idan Allah ya yarda zan yi abinda mutanenmu za suyi alfahari dani da kuma Jam’iyyarmu ta APC.
Muktar ya kara da cewa, ya tsaya takara ne domin ya taimakawa al’umma ta hanyar kawo kudirori wanda zai taimakawa musu kuma idan mutum ya damu da al’ummarsa wajen kulawa da dasu yau da kullum zai zamu goyon bayansu wanda a halin yanzu yake samu.
” Idan aka zabe ka sannan ka nisanta kanka da mutanen ka, zasu ɗauka baka tare dasu. A halin yanzu, duk da cewa Muhammad Gudaje ya fice daga Jam’iyyar APC kuma yana takara da ni, ban daukarsa a matsayin babban abokin hamayya.
” Al’ummarmu suna hasara wajen cin moriyar manyan ayyuka daga gwamnatin tarrayya, wanda ya kamata M Gudaje ya kawo musu amma bai yi ba, idan aka zabe ni zan kawo canji wajen kawo manyan ayyuka a mazabar Kazaure.
Discussion about this post