Kazeem Ganiyu ya zama abin tausayi bayan ya rufe gidan biredin sa a unguwar Muslim-Odinjo da ke cikin Ibadan, tun a cikin watan Fabrairu.
“Filawa ta yi tsada, sukari ya yi tsada, Kai komai ya yi tsada. Mun rage hannu kwastomomi sun ƙi saye, sun ce biredin ya yi ƙanƙane. Ba mu komai sai tabka asarar da ko albashin ma’aikata ba ni iya biya. Sai kawai na rufe gidan biredin.” Haka ya shaida wa PREMIUM TIMES a wata tattaunawa da wakilin mu ya yi da shi.
Daga Fabrairu zuwa Agusta 2022, bayan Kazeem ya rufe gidan biredin sa, an rufe dubban gidajen biredi a faɗin ƙasar nan, kama daga Kano, Katsina, Kaduna da sauran garuruwan Arewa da Kudu baki ɗaya.
Sauran gidajen biredin da ba su rufe ba kuwa, to ɗayan biyu, ko dai manyan gidajen biredi ne waɗanda masu hali ke saye komai tsadar sa, ko kuma game-gari ne wanda ake haɗawa har da garin nasara, a ci maganin yunwa, ba don daɗi da gamsarwa ba.
Cikin watan Maris Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa za’a yi fama da ƙarancin abinci a Najeriya, inda mutum kimanin miliyan 20 za su yi fama da ƙarancin abinci a Najeriya, tsakanin Yuni zuwa Agusta.
Daga nan sai Ma’aikatar Harkokin Noma da Bunƙasa Karkara ta Tarayya ta danganta matsalar da za ta faru da hare-haren ta’addanci na Arewa maso Gabas a Yobe, Barno da Adamawa da kuma farmakin ‘yan bindiga a Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Benuwai, Kaduna da irin su Neja.
Sannan kuma wata babbar matsalar ita ce tsadar kayan abincin su kan su baya ga ƙarancin su.
Yaƙin Rasha da Ukraniya ya haifar da tsadar sukai nau’in kayan abincin da ake shiga ƙasashe da su daga ƙasashen biyu.
Sannan kuma kayan abincin da ake sayowa a wasu ƙasashen, sun yi ƙaranci, saboda manyan jiragen ruwa na jin tsoron ketawa yankin da ake gumurzun yaƙi, kada farmaki ya ritsa da su.
Sannan kuma kashi 90 bisa 100 na alkamar da ake fita da ita daga Ukraniya zuwa ƙasashen duniya, duk Rasha ta hana fita da ita.
Wannan lamari ya ƙara haifar da tsadar wasu kayan abinci a duniya, yunwa da kuma tsadar rayuwa. Saboda Rasha ta hana kowane jirgin ruwa na duniya keta ‘Black Sea’ ya ɗauko kaya.
Dama a wasu kasashen da dama irin su yankin Gabas ta Tsakiya, Afrika ta Arewa da wasu sassan Asiya, tsadar kayan abinci ta rigaya ta yi katutu, tun ma kafin ɓarkewar yaƙin Rasha da Ukraniya.
A Najeriya, baya ga matsalolin da ake fuskanta, masu shigo da kaya daga waje na fama da tsadar biyan harajin shigo da kaya cikin ƙasa, wato ‘import duties’, wanda hukumar kwastsn ke karɓa a kan mizanin tsadar kaya, ba kan nau’in kaya ba.
Wata babbar matsalar da ke addabar masu masana’antun sarrafa kayayyaki, musamman na abinci ita ce matsalar ƙarancin wutar lantarki. Cikin 2022 babbar tashar samar da ƙarfin wuta ta ƙasa ta durƙushe sau biyar. Wasu ma na cewa sau bakwai.
Sannan kuma sai uwa-uba matsalar faɗuwar darajar naira ƙasa warwas, shi ma ya ƙara dagula matsalar, wadda har yanzu babu wata alamar mafita.
Discussion about this post