Kakakin Majalisar Kamfen ɗin APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Festus Keyamo, ya bayyana cewa Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP ne ƙasa ga Bola Tinubu da Peter Obi wajen cancanta ta tasirin iya ɗaukar mataki a matsayin sa na shugaba.
Ya yi wannan magana a wata hira da aka yi da shi a gidan Talbijin na Channels TV, ranar Juma’a.
Keyamo ya ce Atiku bai taɓa riƙe wani muƙamin da za a ce shi ne zai zartas da wani hukunci ko umarni ba na jagorancin jama’a.
“Amma Bola Tinubu da ke wa APC takarar shugaban ƙasa da Peter Obi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, duk sun taɓa riƙe muƙamin gwamna.
“Shi kuma Atiku an zaɓe shi gwamna a jihar Adamawa cikin 1999, amma kafin a rantsar da shi, sai Obasanjo ya ɗauke shi takarar mataimakin shugaban ƙasa.” Inji Keyamo.
Keyamo wanda shi ne Ƙaramin Ministan Ƙwadago, ya ce ba a taɓa jaraba Atiku har an gamsu da zurfin tunanin ƙwarewa da gogewar sa wajen iya mulki ba. Don haka ta yaya za a zaɓe shi ya shugabanci Najeriya?
Da ya matsa gaba, Keyamo ya kare gwamnatin Buhari, inda ya ce har gwamnatin Buhari ta fi gwamnatin Amurka iya taka-tsantsan a lokacin tsadar rayuwar tattalin arzikin ƙasa.
“Ya ƙara da cewa Najeriya ta ma fi Amurka, Canada, Spain da Jamus.”
“Sai raggo zai tsaya ya na kamfen da farashin tumatir. Me ye tumatir, idan ana maganar tattalin arzikin duniya. Ban ce wai Najeriya ta yi rawar gani sosai matuƙa a lokacin da ake fama da tsadar rayuwa ba. Amma idan ana maganar duniya, to mun ɗara Amurka, Canada, Spain, Rasha da Jamus.”
Batun tsaro kuma ya ce Gwamnatin Buhari ta fi gwamnatin baya yin ƙoƙarin wajen kakkaɓe Boko Haram da ‘yan bindiga.
Batun matsalar tsaro a Abuja da kewaye kuwa, Keyamo ya ce duk jaridu ne ke zuzuta batun amma bai kai ya kawo yadda ake tunani ba.