Jami’an tsaro dake aiki a yankin dazukan da ke kewwaye da jihar Kaduna sun yi nasarar dagargaza maɓoyan ‘yan bindiga inda suka ceto mutane da dama sannan suka fatattaki wasu maharan suka arce cikin daji bayan waɗanda suma kama da waɗanda suka aika lahira.
Bisa ga sanarwar da kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan ya fitar tun daga ranar Laraba inda ya ke yi wa manema labarai karin haske game da bayanan da rahotanni rundunonin tsaro da ke aiki a jihar ya ce “Bisa ga rahoton da gwamnati ta samu dakaru dake aiki a yankin jihar sun dagargaza wasu ƴan bindiga da suka bi su har maɓoyan su a tankin ƙaramar hukumar Chikun suka kashe wasu sannan suka ceto wasu mutane shida da suka yi garkuwa da su.
Mutanen da jami’an tsaron suka ceto sun hada da Sahura Hamisu, Ramlatu Umar, Saudatu Ibrahim, Maryam Shittu da Fatima Shuaibu da Khadijah Mohammed da danta da take goyo.
Bayan haka Aruwan ya ce gwamnati ta samu rahoton cewa jami’an tsaron ‘Operation Safe Haven’ sun kama mutum 7 da ake zargin ‘yan bindiga ne a kauyen Mariri dake karamar hukumar Lere.
Maharan da aka cafke sun haɗa da wani mai suna Musa Adamu, da Abdullahi Usman, sai kuma Suleiman Hasidu, da Usman Jibril, da Saidu Isah, Hassan Abdulhamid sai kuma na karshe mai suna Idris Sani.
“Gwamnati ta kuma samu labarin wasu mutane sun babbake wata mata mai suna Hajiya Bilkisu da suka kama da laifin bai wa maharan wurin zama.
Ya ce gwamnati ta jinjina kokarin da jami’an ayyukan da jami’an tsaron suke yi a yankunan jihar.
Haka kuma a ranar Alhamis, dakarun tsaron sun kau wa gidan wani ƙasurgumin ɗan bindiga wanda da mai suna Lawal Kwalba, wanda ke zaune a yanki. ƙaramar hukumar Chikun.
Duk da dai ba a same shi ba, sojoji sun babbake gidansa sannan an kwashe buhannan taki, wayoyi da batira da ake zaton da su suke haɗa bam.
Bayan haka kuma an bi wasu har cikin ƙungurmin daji inda aka kamo wasu mutum shida suna wanda ake zargi duk ƴan bindiga ne masu yin garkuwa da mutane.
Discussion about this post