Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Sandamu/Daura/Mai’aduwa, Fatuhu Muhammad, wanda ɗan wan shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya fice daga jam’iyyar APC.
Sanarwar ficewa daga jam’iyyar APC ya bayyana a yau Lahadi inda ya aika wa gundumar mazaɓar sa da wasikar ficewa daga jam’iyyar.
Fatuhu ya yi barazanar ficewa daga APC tun bayan bayyana sakamakon zaɓen fidda gwani da aka yi wanda ya ce an yi masa rashin adalcin wajen kifar da shi a zaɓen.
Wani mai suna Aminu Jamo ne ya kayar da Fatuhu da ƙuri’u 117, shi kuma Fatuhu ya samu ƙuri’u 30 kacal.
A cikin wata magana da Fatuhu ya yi ta waya, shi da wani kuma aka riƙa watsa rikodin ɗin maganar, Ɗan Majalisar ya yi iƙirarin cewa fashi aka yi masa, kuma sai ya ƙwato haƙƙin sa, ko kuma ya fice daga jam’iyyar.
Hirar wadda ke da tsawon minti 6 da sakan 22, PREMIUM TIMES ta saurari inda Fatuhu ke magana da wani da ya ke kira Ranka Ya Daɗe, ya na ce masa sai ya tarwatsa APC a Jihar Katsina.
Ya ce shi ba zai tsaya sake wani zaɓen fidda gwani ba, ko ma da jam’iyya ta ce a sake ɗin. Saboda shi ne wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin da aka yi, amma aka danne masa.
“Ba za su iya sake wani zaɓe ba. Saboda ni na yi nasara a zaɓen farko da aka yi. Sun karya doka. Don haka a ba ni takara ta. Ko mu haɗu a kotu, ko kuma na tarwatsa APC, na kawo wata jam’iyya a Daura.” Inji shi.
“Zan fa iya rungumo jam’iyyar nan ta Kwankwaso mai kayan marmari na kai ta a Daura.
Sai dai kuma hadimin ɗan majalisan Ahmed Ganga ya ce Fatahu ya gana da Atiku amma kuma bayyana ko zai koma PDP ba.
Idan komawarsa PDP ya tabbata, zai kasance duka masu wakiltar shiyyar Dauran Buhari a majalisun dokokin kasa duk basu jam’iyya ɗaya da Shugaban Kasa kenan.