Fadar gwamnatin Muhammadu Buhari ta soki ƴan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna cewa basu da Alkawari.
Kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana cewa sun yi alkawari da ƴan bindiga cewa gwamnati za ta saki wasu ƴaƴan su da mata da ke tsare a kurkukun gwamnati.
” Alkawarin shine zamu saki wasu matayen su da ƴaƴan su da aka kama, amma kuma sun yi alkawarin za su saki duka fasinjojin da suka yi garkuwa da su.
” Bayan mu mun cika namu alkawarin mun sakan musu mata da ƴaƴayen su sai suka canja baki, suka ki sakin mutanen suka ce sai gwamnati ta biya wasu maƙudan kudade.
Rahotanni sun nuna duk wanda ƴan ta’addan suka saki sai da ya biya miliyoyin naira kafin suka sake shi.
Har yanzu akwai fasinjojin dake tsare a hannun ƴan ta’addan wanda ba a san ranar sako su ba.
Discussion about this post