A kauyen Dabai ne dake karamar hukumar Gwale jihar Kano wasu ‘yan banga suka kashe malami da duka bisa zargin wai ya saci jaririn wata mata.
Mazauna kauyen sun ce Musa Mai-Almajirai Malami ne dake da makarantar almajirai da yake koyar da su.
Dan mamacin Ibrahim ya bayyana wa jami’an tsaro ranar Litini da safe cewa a ranar Lahadin mahaifinsa Malam Musa a hanyarsa kusa da wani bola da ake tzubar da shara ya ji kukan jariri a wurin.
Ya ce da ya duba sai ya ga jaririne aka jefar a wurin ya ya garzaya ya dauko shi. Sai dai kafin ya tafi da wannan jariri ga hukuma sai wata mata ta tsala Ihu cewa wai Malam musa ya sace mata jariri.
” Daga nan sai ‘yan banga suka garzayo suka fara jibgar sa sanna suka waske da shi ofishin su.
Ibrahim ya ce an yi gaggawar kaishi asibiti amma ya rasu ya rasu a hanyar sa ta zuwa asibiti.
Rundunar ‘yan sandan jihar sun kama kwamandan ‘yan bangan kauyen Munkaila sun tsare shi a ofishin ‘ya sanda dake Rijiyar Zaki.
An damka wa dagacen kauyen wannan jaririn.
Discussion about this post