Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta bayyana cewa ta kama wani mahaifi, likita da ma’aikaciyar jinya da ake zargi da laifin siyar da jaririn wata uku akan Naira 400,000.
Kakakin rundunar Benjamin Hundeyin ya sanar da haka a shafinsa na Tiwita ranar Juma’a.
Hundeyin ya ce hakan ya auku ne a kauyen Oko-Oba dake jihar.
“Rundunar ta kama wadannan mutane bayan ƙaran da mahaifiyar jaririn ta kawo ofishin ƴan sanda game da bacewar jaririn ta.
“Sakamakon binciken da ƴan sanda suka yi ya nuna cewa mahaifin jaririn ne ya hada baki da likita da jami’ar jinya domin siyar da jaririn wa wata mata akan naira 400,000 ba tare da sanin mahaifiyar dan ba.
Ya ce da idan fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka ta kammala gudanar da bincike za a kai wadannan mutane kotu.
Bayan haka kuma rundunar ta bayyana cewa ta kama wata mata mai shekaru 23, wanda ta sai da jaririn ta akan naira ₦600,000.
Satin jaririn uku da aka saida
Discussion about this post