Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya ƙalubalanci tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmed Makarfi da ya dai na cika baki ya na tsoma bakin sa a harkar da bai shafe shi, ya rika kantara mafana son ransa bayan Kadunar ma ta gagareshi.
Makarfi ya yi kira ga Wike ya rika sara ya na duban bakin gatarin sa irin kalaman da ya ke yi da kuma rashin jituwarsa da jigajigan jam’iyyar PDP har da ɗan takarar jam’iyyar, Atiku Abubakar.
Sai dai kuma Wike ya maida masa da martanin cewa idan yana so yayi magana ya kawo wa jam’iyyar PDP jihar Kaduna a zaɓe mai zuwa.
” Ba mu son mu ji wai ai an yi mana murɗiya ne, ga jihar Kaduna nan, ya kawo ta mana mugani ba yana ji shi jigo bane a jam’iyyar. Wannan shine magana, ba wai sai wasu su rika dogaro da wani yankin, su kuma jihohinsu sun gagaresu ba.
Wike ya kara da cewa ƙalubale ne ga duk masu cika baki a PDP su je su ciwo jihohin su tukunna.
” Ku kawo wa PDP Kano, Katsina, Kaduna, Jigawa da sran jihohin ku, ba ku riƙa raɓe wa a gefe ba kuma dogaro da kuri’un wasu yankunan sannan kuma kuna masu cika baki.
Akarshe ya ce Makarfi ya daina saka bakin sa a cikin abin da babu ruwan sa a ciki ya je can ya gama da nashi kalubalen tukunna.
Discussion about this post