Ɗan Majalisar Tarayya Solomon Rob daga Jihar Ribas, ya bayyana cewa wasu ‘yan barandar jikin Atiku Abubakar ne ya haɗa shi rashin jituwa tsakanin sa da Gwamna Wike.
Da ya ke amsa tambayoyi a gidan talabijin na Channels, Rob ya ce, “ƙarairayi da tuggun da makusantan Atiku Abubakar su ka riƙa fesawa kafin zaɓen fidda-gwani da bayan kammala zaɓen ne su ka haddasa rashin jituwa da rashin fahimta tsakanin Atiku da Wike.
“Sun riƙa fesa waɗannan ƙarairayi don kawai su ɓata takarar Wike, kuma su aibata shi bayan ya faɗi zaɓen don kada ya zama mataimakin takara.
Rob ya ce, “da su ke cewa Wike na jin haushin Atiku don bai ɗauke shi ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ba, ƙarya su ke yi, Wike bai faɗi haka ba.
“Kuma shi Wike tun farko takarar shugaban ƙasa ya nema, domin ya na da ajandar sa ta idan ya yi nasara, to ga irin gyaran da zai yi wa matsalolin da su ka addabi Najeriya.”
Rob ya kuma zargi shugabannin PDP na ƙasa da kantara wa Wike ƙarairayi.
Ya ce da ‘yan jagaliyar Atiku ba su yaɗa ƙarairayi kan Wike ba, to da ba a samu wawakeken giɓi tsakanin Wike da Atiku ba.
Ƙoƙarin Sasanta Wike Da Atiku:
Atiku da Wike sun amince a kafa kwamitin mutum 14 su shata sharuɗɗan daidaitawar su.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike sun amince cewa kowa a cikin su zai bayar da sunayen mutum bakwai, domin a kafa kwamitin da zai shata sharuɗɗan daidaitawar ɓangarorin biyu.
An cimma wannan yarjejeniyar ce a taron da Atiku da Wike su ka yi ranar Juma’a, a gidan Jerry Gana, a Abuja.
Wannan ne karo na farko da manyan masu rashin jituwar a PDP su ka haɗu, tun bayan kammala zaɓen fidda-gwanin ‘yan takarar PDP, wanda Atiku ya zo na farko, Wike ya zo na biyu.
PREMIUM TIMES dai ta tabbatar cewa nan cikin sa’o’i 48 aka ce za a kafa kwamitin, amma ba ta tabbatar da sunayen da Atiku ya bayar ba, ko kuma sunayen da shi ma Wike ya bayar a kwamitin ba.
An tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran Atiku, Paul Ibe, amma bai maido amsa ba.
Sun zargi cewa har ma makusantan Atiku sun raba manyan muƙaman gwamnati a tsakanin su, tun ma kafin zaɓen 2023 ɗin ya zo, ba a ma kai ga cin narasa ba.
“Ta yaya ɗan takarar da ke haka tun a yanzu za a yi tsammanin zai canja idan ya zama shugaban ƙasa kuma?”
Aƙalla mutum 51 ne su ka halarci taron, ciki har da gwamnoni biyar, tsoffin gwamnonin PDP bakwai.
Akwai Suleiman Nazifi da tsohon Antoni Janar Mohammed Adoke. Sai Hosea Agboola, Phillip Aduda, Zainab Kure, Garba Lado, Sunday Onoh da sauran su.
Akwai kuma Mohammed Abacha da sauran su.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Wike ya karɓi baƙuncin Gwamnonin PDP na yanzu da na da can.
Yayin da rashin jituwa tsakanin Gwamna Nysome Wike na Jihar Ribas ke ƙara haifar da ɓaraka tsakanin sa da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar, Gwamnonin PDP sun kai masa ziyara a ranar Lahadi.
Gwamnonin sun kai ziyarar ce kwana ɗaya bayan da manyan ‘yan tawayen APC, Yakubu Dogara da Babachir Lawal sun kai masa ziyara, jim kaɗan bayan dawowar sa daga bulaguro a ƙasar waje.
Gwamnonin da su ka kai wa Wike ziyara, sun je ne tare da wasu tsoffin gwamnonin PDP, inda a ranar Lahadi su ka gana da shi a asirce, a Gidan Gwamnatin Jihar Ribas da ke Asokoro, Abuja.
Ba a san dai abin da su ka tattauna ba. Amma kuma tabbas tattaunawar ba ta rasa nasaba da saɓanin da ke ƙara tsanani tsakanin Wike da Atiku Abubakar.
An samu saɓani tsakanin manyan jiga-jigan PDP ɗin biyu, tun bayan kammala zaɓen fidda-gwani, inda Atiku ya yi nasara, shi kuma Wike ya zo na biyu.
Tun bayan kammala zaɓen dai Wike ya yi tsinuwa da Allah–wadai ga wasu manyan jam’iyyar da ya ce sun yi masa butulci, inda ake ganin da Gwamna Aminu Tambuwal ya ke, wanda ya janye kafin zaɓe, ya ce a zaɓi Atiku.
Wike ya kuma ragargaji masu zaɓen ‘yan takara daga Kudu, waɗanda ya ce sun sayar da ‘yancin ‘yan kudu saboda ‘yan kuɗi kaɗan.
Sannan kuma Wike ya ragargaji ɗaukar Gwamna Okowa na Jihar Delta matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ga Atiku.
Daga baya Wike ya ce Atiku ya yaudare shi, domin bayan kammala zaɓe, ya bi Wike ɗin har gida ya ba shi haƙuri. Kuma ya ce shi zai ɗauka mataiakin takara.
Ɗaukar Okowa ya fusata Wike, inda ya riƙa fesa wa Atiku munanan kalamai, kuma har yau bai taya Okowa murnar zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP ba.
Kwanan nan Atiku ya fito ya ce masu ba shi shawarar wanda zai ɗauka mataimakin takara, ba su ba shi sunan Wike ba. Wannan furuci daga Atiku ya harzuƙa Wike, har ya kira Atiku ƙasurgumin maƙaryaci.
Gwamnonin da su ka ziyarci Wike sun haɗa da: Seyi Makinde na Oyo, Samuel Ortom na Benuwai, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Okezie Ikpeazu na Abiya.
Tsoffin gwamnonin sun haɗa da Donald Duke na Cross River, Gabriel Suswan na Benuwai, Olusegun Mimiko na Ondo, Ibrahim Idris na Kogi da Johan Jang na Filato.
Jiga-jigan PDP sun fara ɗar-ɗar da Wike tun bayan da gwamnonin APC uku daga Kudu maso Yamma su ka kai masa ziyara. Sai kuma ziyarar da Yakubu Dogara da Babachir Lawal su ka kai masa a ranar Asabar.
An ruwaito Wike dai na cewa ba zai fita daga PDP ba.
Discussion about this post