Wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC da suka hada da gwamnan Legas, Sanwo-Olu, na Ondo, Rotimi Akeredolu da gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi zasu kai ziyarar gaisuwa ga gwamnan jihar Ribas Nysome Wike.
Ko da yake shugaban gwamnan Ekiti, kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ya bayyana cewa ziyarar ba ta siyasa bace, akwai sahihan bayanai dake nuna cewa ziyara ce ta neman goyon baya.
Duka gwamnonin makusantan ɗan takarar shugaban kasa ne na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, wanda ake ganin zaiyarar na neman goyon baya ne domin zaben 2023.
Jam’iyyar PDP ta afka cikin ruɗani da mawuyacin hali tun bayan zaɓen gwamnan Delta Okowa da Atiku Abubakar yayi a matsayin mataimakin sa.
Mafi yawa daga cikin jigajigan PDP, sun karkata ne zuwa Wike wanda suke ganinya kamata jam’iyyar ta saka masa bisa irin gudunmawar da baiwa jam’iyyar da kujerar mataimakin shugaban kasa.
Amma kuma sai Atiku yayi gaban kansa ya ya zaɓi gwamnan Delta Okowa a matsayinsa n maraimakin sa
Gwamnoni irin su Emmanuel Ortom na Benuwai da wasu jigajigan PDP duk sun bayyana rashin jin daɗinsu da abinda ya faru na zaɓin Okowa.
Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya ziyarce shi, a kwanakin baya, haka kuma shima Peter Obi na jam’iyyar LP ya ziyarce shi.
Ga dukkan alamu dai kowa na zawarcin sa ne fomin samun goyon bayan sa su yi nasara a zaben shugaban Kasa.
Discussion about this post