Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zaɓen 2023 zai kasance wani babban darasi da misalin ƙara wa dimokraɗiyya kandagarkin hana yi mata karan-tsayen juyin mulki a Afirka.
Buhari ya bayyana haka a jawabin sa wajen Taron Ranar ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje, wanda aka yi a Abuja.
Buhari wanda Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari ya wakilta, ya ce ya sha nanata cew, “wannan muradi na ne da kuma muradin gwamnati na ga na ajiye kyakkyawan tarihin yin zaɓe mafi karɓuwa kuma mafi inganci, wanda zai zama kandagarkin hana dimokraɗiyya zaizayewa a Afirka.”
Buhari ya jinjina wa ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, waɗanda ya ce sun kai mutum miliyan 17. Ya ce ya na alfahari da kasancewar su jakadu nagari.
Da ta ke jawabi, Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje, Abike Dabire-Erewa, ta ce taron ba na ganawa a sha shayi a tashi kawai ba ne. Ta ce za a tattauna batutuwa masu muhimmancin gaske.
A wani labarin kuma, INEC ta sha alwashin zaɓuɓɓukan 2023 za su fi na baya inganci.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bada tabbacin cewa manyan zaɓuɓɓukan da za a yi a Nijeriya a baɗi sai sun fi duk waɗanda aka yi a baya nagarta.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya faɗi haka a ranar Talata a Abuja lokacin da ya karɓi baƙuncin jami’an wasu hukumomin tsara harkar zaɓe da su ka zo daga Amurka, wato ‘International Republican Institute’ (IRI) da
‘National Democratic Institute’ (NDI).
Ya ce zaman da su ka yi da maziyartan shi ne na karo na farko da INEC ta karɓi baƙuncin wasu masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe tun bayan zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka yi a ran Asabar, kuma ya yi alƙawarin hukumar za ta ɗora a kan nasarorin da ta samu a zaɓuɓɓuka masu zuwa.
Farfesa Yakubu ya faɗa wa maziyartan nasa cewa: “Kyawawan kalaman ku sun ƙara mana ƙwarin gwiwa, amma har yanzu akwai babban aiki a gaban mu.
“ Mu na ba ku tabbacin cewa za mu ci gaba da aiki tuƙuru fiye ma da na da domin gudanar da manyan zaɓuɓɓukan 2023.
“Na saurari wasu daga cikin batutuwan da aka gabatar a nan, amma ƙila idan mun shiga zaman aikin da za mu yi akwai damar da za mu samu mu yi tsokaci kan wasu daga cikin batutuwan.’’
Yakubu ya kuma yi magana kan zaɓuɓɓukan gwamna da aka yi a Ekiti a watan Yuni da na Osun da aka yi a ranar Asabar.
Ya ce: “Dangane da shirin manyan zaɓuɓɓukan 2023, ina so in tabbatar maku da cewa sai da mu ka yi wa ‘yan Nijeriya alƙawarin cewa zaɓen Ekiti zai yi kyau, kuma sai ga shi zaɓen na Ekiti ya yi kyau. Mun yi alƙawarin zaɓen Osun zai ma fi kyau, sai ga shi zaɓen na Osun ya yi kyau fiye da wanda ya gabace shi.
“Yanzu mu na maku alƙawarin cewa manyan zaɓuɓɓukan 2023 za su fi duk wani zaɓe da mu ka yi a baya inganci kuma mun sadaukar da kan mu wajen gudanar da zaɓe mafi nagarta.”
Tun da farko, sai da jagoran maziyartan, Mista Frank LaRose, wanda shi ne Sakataren Jihar Ohio ta ƙasar Amurka, ya yaba wa INEC kan ƙoƙarin da ta ke yi na inganta al’amarin zaɓe a Nijeriya.
LaRose, wanda kuma kwamishinan zaɓe ne a Jihar ta Ohio, ya bayyana wannan ziyara da ya fara kawowa a Nijeriya a matsayin wata babbar dama da ya samu ta koyon abubuwa. Ya yi kira ga INEC da ta ci gaba da inganta tsarin zaɓe na Nijeriya.
Ya ce: “Ina jagorantar maziyarta waɗanda manyan masana ne a harkar zaɓe daga yankin mu, da ma faɗin Amurka.
“Waɗannan maziyartan su na da tunani irin naku na cewa mutanen Nijeriya sun cancanci su ci gaba da samun zaɓe mai inganci babu murɗiya, karɓaɓɓe ga kowa, saboda haka mu na aiki domin shirya wa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.
“Mun samu damar kai ziyara a Osun saboda wannan shi ne karo na biyu da aka gudanar da zaɓe a ƙarƙashin sabuwar Dokar Zaɓe.
“Mun haɗu da Kwamishinan Zaɓe Mazaunin can (REC) a Osun kuma mun yi nazarin wuraren kaɗa ƙuri’a daban-daban a Ranar Zaɓe.
Discussion about this post