‘Yan ta’addar da su ka kai hari kan jirgin ƙasa tsakanin Abuja da Kaduna, har su ka yi har garkuwa da sama da mutum 60, sun saki wani sabon bidiyo.
A cikin bidiyon, an nuno su na jibgar wasu daga cikin waɗanda ke tsare a hannun su da sanduna, har su na kukan neman ceton su.
Lamarin ya yi muni har wani daga cikin ‘yan bindigar ya nuna ɓacin rai da tausayin dukan da ya ga ana yi masu. Daga nan sai ya kira masu dukan, Ali da Abdullahi, ya ce su daina dukan waɗanda ake tsare da su ɗin.
Daga nan sai aka nuno wani daga cikin fasinjojin ya na bada labarin yadda aka kama su, kuma ya ke nuna damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ta yi watsi da su, ta kasa ceto su.
Fasinjan da ke tsare ɗin ya roƙi gwamnatin Amurka, Birtaniya da ta Faransa su kai masu ɗaukin ceto su daga hannun waɗanda ke tsare da su.
Ya ce ‘yan bindigar ba su yi niyyar riƙe su har tsawon lokaci a cikin daji.
Wata matar da ita ma ake tsare da ita, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya tare da kiran gwamnatin Buhari da suna “muguw”.
Wani daga cikin ‘yan ta’addar ya ce Gwamnatin Najeriya za a ɗora wa laifin abin da ke faruwa da waɗanda su ka tsare ɗin, saboda gwamnatin ta ƙi yin abin da su ke nema a yi masu.
“Ai mun san shirin da Gwamnatin Najeriya ke yi wai don su kuɓutar da mutanen da ke tare da su a dajin.
“To Gwamnanti ta sani idan ba ta biya mana buƙatar mu ba, wannan wurin zai zama mayankar mutane kawai.” Cewar ɗan ta’addar.
Mutumin wanda kusan kamar shi ne shugaban gungun maɓarnatan, ya sha alwashin cewa sai sun damƙi manyan jami’an gwamnati, manyan ‘yan siyasa da sanatoci.
Duk da cewa an saki wasu fasinjojin da ake tsare bayan an biya maƙudan kuɗaɗe, har yanzu akwai sauran mutum 43 a hannun su, ciki har da ɗan Idris Garba, tsohon Gwamnan Kano na mulkin soja, da matar sa da ‘ya’yan sa, duk su na hannun maharan.
Cikin watan Yuni Shugaba Muhammadu ya umarci manyan jami’an tsaron Najeriya cewa su yi duk wani abin da ya zama dole su ceto waɗanda ke hannun ‘yan ta’addar.
Sai dai kuma har yanzu shiru ka ke ji.