‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya hudu a kauyen Nise dake karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra.
Maharan sun yi garkuwa da mutanen da misalin karfe 3 na yamman Lahadin da ya gabata a kasuwar kauyen dake kusa da gidan gwamnan jihar Charles Soludo dake kauyen Amawbia.
‘Yan bindigan sun kuma yi wa wasu daga cikin matafiyan fashi sannan suka cinna wa daya daga cikin motocin matafiyan wuta.
Maharan sun yi wa mazauna kauyen dake wucewa fashi sannan suka gudu a wata mota kira SUV wanda ake zargin na daya daga cikin matafiyan da suka yi wa fashi ne.
Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Tochukwu Ikenga ya tabbatar da haka sai dai ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da mutum daya ne kawai.
Ikenga ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bada umurnin farautar maharan domin kamo su da ceto mutanen da suka yi garkuwa da su.
Tabarbarewar tsaro a yankin Kudu maso Gabas
Rashin tsaro na kara tabarbarewa a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.
Jihar Anambra na daga cikin jihohin dake fama da hare-haren ‘yan bindiga a yankin.
Idan ba a manta ba watanni uku da suka gabata ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum uku ‘yan daurin aure a kauyen Akpo dake karamar hukumar Aguata.
Gwamnati na yawan zargin kungiyar Biafra/IPOB da kai wa mutane, jami’an tsaro da gine-ginen gwamnati hari amma kungiyar na musanta haka.
Shugaban kungiyar Biafra/IPOB na tsare a hannun jami’an tsaro a Abuja bisa laifuffukan da suka hada da cin amanar ƙasa, yi wa ƙasa zagon-ƙasa, maƙarƙashiya da kuma ayyukan ta’addanci.
Discussion about this post