‘Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai wa kauyen Gatagawa dake karamar hukumar Kankara a jihar Katsina hari inda suka kashe ‘yan sanda biyar da wasu mutane uku.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gambo Isa ya tabbatar da haka wa manema labarai ranar Alhamis.
Wata majiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun fatattaki mazaunan kauyen inda suka arce can cikin daji.
“Maharan sun kashe tsofaffi uku da suka kasa arcewa.
Ya ce mutane da dama sun ji rauni a dalilin harin kuma maharan sun sace dabbobi da dama daga wannan kauyen.
“Wadanda suka ji rauni na kwance a asibitin Kankara likitoci na duba su.
Bayan haka Isa ya ce ‘yan sandan da maharan suka kashe ma’aikata ne daga rundunar ‘yan sandan jihar Kano da aka turo su jihar Katsina domin yin aikin musamman.
Ya ce daya daga cikin ‘yan sandan da ‘yan bindigan suka kashe mobal ne.
Isa ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin kamo maharan.
“Maharan sun Kai mutum 300 dauke da manyan makamai da suka kai kauyen hari da misalin karfe 6:45 na yamma.
Hare-haren ‘yan bindiga ya tsananta a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.
Mahara na yin garkuwa da mutane, sun hana mutane noma a yankin sannan suna sace wa mutane dabbobi.