Yadda ‘yan bindiga suka kashe direba da fasinboji 4 suka sace matafiya da dama a Katsina
‘Yan bindiga sun kashe direban motar gwamnati ta KTSTA dake dauke da fasinjoji da wasu matafiya hudu dake cikin wannan mota kirar Bus, sannan sun sace wasu da dama daga cikin wannan mota.
‘Yan bindigan sun dira wa motar ne da misalin karfe 11 na safe a Mil Takwas da kauyen Farun Bala wanda ke kusa da barikin Sojoji dake Katsina.
Wani magidanci mai suna Nasir Mohammad ya bayyana cewa matarsa na daga cikin fasinjojin dake ke cikin wannan mota.
” Matata ta kirani ta waya cewa gashinan fa ‘yan bindiga sun tare hanya kuma sun bude wa motarsu wuta. Ta ce kafin su kai ga motar su sun tare wasu motoci har guda hudu.
Mohammed ya ce matarsa ta taso daga Jibia ne za ta zo Katsina inda ya ke aiki.
Haka nan shima shugaban karamar hukumar Jibia ya bayyana cewa an sanar masa cewa ‘yan bindiga sun kwararo wannan hanya, amma kuma kafin ya sanar wa jami’an tsaro da ‘yan banga sun aikata abinda za su yi.
Discussion about this post