Yayin da duniya ta dawo kan tafin hannun duk wani mai amfani da wayar GSM, ba a bar Olarunbosun Olawoye a baya ba, domin shi ma ya mallaki wadda ya ke sanin abin da duniya ke ciki, inda ya ke amfani da Tiwita, Facebook da sauran kafofin sada zumunta.
Ya ce ya na so ya ƙara samun laƙanin gogewar fasaha ta yadda zai riƙa bunƙasa tattalin arzikin da ta amfani da waya.
Sai dai kuma ya yi kukan cewa kasancewa a garin Ile-Ogbo ya ke inda babu wasu ababen sauƙaƙe wahalhalun sadarwa, ya na fuskantar matsaloli da dama na ababen da ba zai iya yi ba.
“Babu ATM ko ɗaya a garin Ile-Ogbo, dama kuma garin har matsalar ruwa duk ana fama da ita.
“To ka ga irin waɗannan matsaloli na dakushe wa mutum kaifin samun nasibin inganta rayuwar sa. Haka nan kuma babu banki ko ɗaya a Ile-Ogbo.”
Garin Ile-Ogbo garin manoma ne da ke kusa da Iwo cikin Jihar Osun. Can ne hedikwatar Ƙaramar Hukumar Aiyedire. Ya na tsakanin Ibadan da Osogbo.
Rashin Uwa A Kan Yi Uwar Ɗaki:
Rashin rumbun ajiyar kuɗi na ATM da bankuna ke yi, da rashin bankuna ya sa jama’ar Ile-Ogbo ba su mu’amala da banki a garin, sai dai wurin cirar kuɗi na P.O.S, wato ‘Point of Sale.’ Shi ake kasuwanci, ciniki, biyan kuɗi da sauran mu’amala da kuɗaɗe da shi.
“Masu POS ne jijiyar sarrafa kuɗaɗe a garin.” Haka wani mai suna Gabriel mai POS ya shaida wa wakilin mu.
“Babbar matsala ita ce, mu ma mu na shan wahala kafin mu samu kuɗin da mu ke yin harkar kasuwancin ta mu. Sai mun je har Iwo kafin mu samu kuɗaɗen da za mu yi sana’ar POS a kullum, saboda a can ne kaɗai ATM da bankuna su ke.”
Ya ce sai ka auna nisa, kasada da matsalar ɓata lokacin da mu ke fuskanta a kullum kafin duk wani mai POS ya ce Iwo ya ciro kuɗaɗe, kowace
rana.
Sama Da Mazauna Karkara Miliyan 42 Ke Fama Da Rashin ATM Da Bankuna A Yankunan Su:
Sama da magidanta miliyan 42 ne ke zaune a yankunan karkara, inda babu hada-hadar bankuna. Haka dai ƙididdigar EFInA ta tabbatar a cikin 2021 a Najeriya.
Saboda haka akwai buƙatar a cike wannan wawakeken giɓi sosai ta hanyar samar wa waɗannan miliyoyin jama’a hanyar amfani da banki ta zamani, domin ragewa da sauƙaƙe masu hanyoyin kyautata rayuwar su ta hanyar hada-hadar kuɗaɗe ta zamani.
EFInA ta ce kashi 71 na mazauna birane na amfani da asusun ajiyar bankuna. Kashi 40 na mazauna karkara na da asusun ajiya.
A kashi 60 na yankunan karkara har yau babu banki kuma ba a amfani da ATM a cikin yankunan na su.
Rahoton dai ya nuna cewa har yanzu kashi 4 ne kacal ke amfani da wayar GSM wajen gudanar da harkokin kuɗaɗe.
Matsalar Ƙarancin ATM Tsadar Harajin Aiki Da Shi:
A cikin 2019 bincike ya nuna a duk cikin mutum 100,000, kashi 8.75 ke amfani da ATM, kamar yadda Bankin Duniya ya tabbatar.
Haɗiyewar da wasu bankuna su yi wa wasu bankuna ta kawo taguwar masu amfani da ATM a ƙasar nan.
Bincike ya nuna cewa mata aka fi bari a baya wajen amfani da ATM a karkara da birane.
Discussion about this post