Akalla mutum 18 ne ‘yan bindiga dake karkashin ikon shahararren dan bindiga Damina suka kashe a harin da suka kai kauyukan Kango da Dangulbi a karamar hukumar Maru jihar Zamfara ranar Lahadi.
Mazauna kauyukan sun ce har yanzu waɗanda suka gudu a lokacin da aka kawo harin basu dawo gida ba.
A jihar Zamfara karamar hukumar Maru na daga cikin kananan hukumomin dake fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Wani basarake a karamar hukumar da baya so a fadi sunan sa saboda tsaro ya ce tuni sun yi jana’izan mutum 18 din da suka mutu a dalilin harin bisa ga karantarwar addinin musulunci.
Wani mazaunin Maru Shehu Ismaila ya ce maharan sun kashe mutum 13 a kauyen Dangulbi da wasu mutum biyar a kauyen Kango.
Ismaila ya ce maharan sun fara kai wa kauyen Kango hari daga nan suka wuce zuwa Dangulbi suka kashe wasu mutane dake aiki a gonakinsu.
“An kashe mutum shida a wajen kauyen sannan mutum bakwai a cikin gari.
“Wadanda aka kashe na daga cikin mutanen da suka tashi da asuba domin su yi aiki a gonakinsu kafin su dawo su ci gaba da shagulgulan sallah.
Ismaila ya ce an dakatar da jana’izan mutanen da aka kashe na ɗan wani lokaci saboda mafi yawan mazauna kauyen sun gudu a lokacin harin.
Bayan haka wani mazaunin kauyen Dansadau Yusuf Abdullahi ya ce harin ya kusa ya ritsa da matar dan uwansa da ta je hutun sallah da goggonta a kauyen Dangulbi.
Ismaila ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa a makon da ya gabata shugaban maharan Damina ya nemi kauyen Dangulbi ta biya shi harajin naira miliyan biyu amma kauyen bata iya biya ba.
Ya ce daga baya dakacen kauyen ya ce sun Yi yarjejeniya da Damina.
Ismaila ya ce a dalilin haka ya sa kowa a kauyen ya saki jiki cewa Damina ba zai kawo musu hari ba saboda yarjejeniyar da suka yi da dagacen.
“Mun zauna tare da Damina da shugaban karamar hukumar inda maharan sun yi alkawarin baza su kawo mana hari ba.
Ya ce maharan sun Kai wa kauyukan hari duk da rokon da kauyukan suka yi da alkawarin da maharan suka yi na dakatar da kai wa kauyukan hari.
“Ban da masaniyar cewa Damina ya bukaci a biya shi naira miliyan biyu domin kada ya kawo hari ba. Mun dai bukaci Damina ya bari mu rika amfani da hanyar Dangulbi zuwa Magami zuwa Gusau amma ya hana.