Gwamnan jihar Ribas Nysome Wike ya yi watsi da wata tawaga da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya aika masa har kasar Turkiyya inda ya ke hutu.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa Atiku ya aiki tsohon ministan ‘Yan sandan Najeriya, Adamu Waziri har kasar Turkiyya inda Wike ke hutu domin ya sanar da shi sakon Atiku amma Wike yayi baza da shi.
Idan ba a manta ba tun bayan zaben gwamnan Delta da Atiku yayi mataimakin sa wike da shi su ka fara zaman doya da manja.
Kafin Atiku ya bayyana dan takarar mataimakin sa sai da shi da kansa ya sa aka kafa kwamiti wanda ya basu damar su zabo masa mataimaki. Kwamitin bayan zama da ta yi a lokutta da dama ta zabi gwamna Wike a matsayin wanda zai yi wa Atiku mataimakin shugaban kasa.
Amma kuma Atiku ya yi watsi ta rahoton kwamitin wanda gwamnan Benuwai ya shugabanta, ya zabi gwamnan Delta, Okowa.
Hakan bai yi musu dadi inda suka fito suka bayyana bacin ransu sannan suka ce ko me Wike yayi yayi daidai.
” Duk a cikin mu ‘yan PDP babu wanda ya rike jam’iyyar yayi mata hidima irin yadda Wike yayi har zuwa nasarar da Atiku ya samu. Kuma bayan an zabi Wike mataimakin shugaban kasa, sai kawai Atiku yayi masa yankan baya ya zabi wani da bam. Akwai rainin wayau a ciki.
Majiya ta ce Waziri ya gamu da Wike a Otel a Turkiyya amma Wike ya ki bashi damar ya ko mika masa hannu su gaisu.
Discussion about this post