Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya zargi dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar da sharara karya game da abubuwan da suka faru a siyasa a baya.
PREMIUM TIMES HAUSA, ta buga labarin yadda Atiku ya yi tir da takarar Muslim-Muslim wanda APC ta yi, cewa APC ba ta yi wa ƴan Najeriya adalci ba
Atiku ya ce ya yi mamakin da APC za ta zaɓi wannan baibawan-burmin siyasa, a ƙasa kamar Najeriya mai mabiya addinai da al’adu ba ɗaya ba.
Haka Wazirin Adamawa ya bayyana a tattaunawa da Gidan Talabijin na Arise TV ta yi shi a ranar Juma’a.
A ranar 10 Ga Yuli ne Bola Tinubu ya bayyana sunan tsohon Gwamnan Jihar Barno, Kashim Shettima a matsayin mataimakin takarar sa.
TInubu da Shettima duk Musulmai ne, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a fagen siyasar Najeriya.
Atiku ya ce batun tikikin Muslim-Muslim shi ne kusan kandagarkin da ya yi masa katanga da Tinubu, shekaru da daɗewa tun ma kafin kafa APC.
Atiku ya bayyana yadda ya ƙi goyon bayan a yi tikitin ‘Muslim-Muslim’, lokacin da zaɓen 20215 ya zo.
“Ni ban yarda a ce daidai ne a ƙasa kamar Najeriya mai ƙabilu da addinai mabambanta, amma a ce wai a fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa duk Musulmai.” Inji Atiku.
Atiku ya ce duk da cewa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na APC wato Shettima a yankin Arewa maso Gabas ya ke, inda Atiku ya fito, duk da haka Atiku ya ce shi ne ya fi alamun yin nasara a zaɓen shugaban ƙasa da za a yi cikin 2023.
Duk da Atiku ya ce Tinubu abokin sa ne, ya ƙara da cewa hakan bai hana ra’ayin su ya bambanta a fagen siyasa.
Bayan haka, Tinubu ya karyata wai Atiku ne ya kafa jam’iyyar ACN, ya ce ba Atiku bane.
” Atiku ya tsinduma ACN ne bayan zama tsakaninsa da Obasanjo shugaban kasa a wancan lokacin ya gagara. An yi watsi da shi a gefe.
” Saboda siyasa Atiku ya koma sai kantara karya yake yi, ya sharara maganganun da basu da asali ko tushe. Ina tabbatar wa Atiku cewa mataimakin da na ɗauka ya fi mataimakin da ya ɗauka sau dubu. Ba za a iya haɗa su ba.
” Ni da mataimakina za mu haɗa kai ne mu gina Najeriya wa Musulmai da Kiristoci ba don wani yana musulmi ba ko kuma kirista ba.
A wannan lokaci da kasar mu ke cikin halin ƙaƙanikayi, dole mu fi maida hankali ne wajen zabo nagartattun shugabanni ba son rai ba.
Discussion about this post