Tsohon sakataren gwamnatin Tarayya, David Babachir ya yi kakkausar martani ga zaɓin Kashim Shettima da dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu yayi na zaɓin Kashim Shettima a matsayin mataimakin sa.
Babachir ya ce Tinubu ya daɓa wa kansa wuka ne a ciki, domin musulmi da ya ɗauka a matsayin mataimaki ba zai haifar far masa da ɗa mai ido ba.
Babachir ya ce ” Ina so Tinubu ya sani cewa zaɓan musulmi da yayi, ya ‘Kwafsa’ domin ba zai yi masa tasirin cin zaɓe ba. Tun daga yin haka ma Tinubu ya faɗi warwas. Da ma Kirista ya zaɓa da ya fi masa.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya wanda harkallar handame wasu kuɗaɗen kwangilar cire ciyawa a Yobe ta lunkume, shugaba Buhari ya fatattaka ya kara da cewa, wasu ne suka yi babakere suka hana kowa kusantar Tinubu domin su dulmiyar dashi ga shi kuma ya dulmiya, idan ko ba sake lale aka yi ba wato a ka canja Shettima, musulmi wani kirista ba ya zama mataimakin Tinubu, APC zata ji a salansa.
A cikin wasikar da Babachir ya rubuta, ya zargi mutane kamar su Ganduje da kulla makininisar da ta sa Tinubu ya zaɓi musulmi mataimaki.
” Ganduje na da wata gidauniya wanda aikin ta shine kawai su rika musuluntar da Kiristoci. Wata ɓoyayyar akidar wannan gidauniya.
Sai dai kuma Ganduje ya maida masa da martanin cewa lallai Babachir ya shiga taitayin sa ya garkame bakin sa tunda wuri.
” Ka sani kai jigo ne a jam’iyyar APC kuma kamar yadda ka ce makusancin Tinubu, bai kamata ace daga bakinka ne irin waɗannan kalamai za su rika fitowa ba har da saƙa addini a ciki.
Ya gargaɗi Babachir da sauran waɗanda suke fushi da lamari da su rika sara suna dubin bakin gari musamman ga al’amuran da suka shafi addini.
Discussion about this post