Dan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na APC shirgegen makaryacine domin ya nemi shi Atuikun ya zabe shi dan takarar mataimakin shugaban kasa su yi Muslim-Muslim a 2007.
Ko da yake Atiku ya ce bai ga laifin Tinubu ba idan ya karyata cewa ya nemi ya zama mataimakin shugaban kasa a 2007, domin akwai yiwuwar akwai matsala a kwakwalwarsa yanzu, ba zai iya tunawa ba tunda ma ya manta jam’iyyar a baya.
Paul Ibe, wanda shine ya saka wa wannan martanin Atiku ga Tinubu hannu ya ce, Tinubu ya ce wai Atiku ne ya nemi ya zama mataimakin sa ba shi ya nemi a yi masa haka ba, shine dalilin da ya sa dole su maida wa Tinubu martani su kuma tunashe shi game da abin da ya faru a baya idan ya manta.
Atiku ya ce akwai bincike da rahotanni da dama da suka bayyana yadda tinubu ya rika bibiyar a nada shi mataimakin shugaban Kasa ba tun yanzu ba.
“Idan ba a manta ba, shi kan sa Tinubun ya karyata cewa ya nemi a yi masa mataimakin shugaban kasa a 2015. Wanda kowa ya sani cewa ya matsa a wancan lokacin amma kuma daga baya ya fito ya ce ba haka bane.
Discussion about this post