Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, ya bayyana cewa ya na sane da irin ƙalubalen da ke gaban sa, saboda ya ɗauki Sanata Kashim Shettima matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
A cikin wata takardar da ya fitar bayan ya bayyana sanar da sunan Shettima a Daura, lokacin da ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyarar gaisuwar Sallah, Asiwaju ya ce ya sha fama da masu cewa lallai Kirista ya kamata ya ɗauka a matsayin mataimaki. A ɓangare guda kuma wasu na cewa Musulmi ya kamata ya ɗauka mataimakin shugaban ƙasa idan ana so a yi nasara.
Tinubu ya ce babban abin dubawa dai shi ne yadda za a yi wa ƙasa da al’ummar cikin ta aiki tuƙuru, ba batun addini ko ƙabila da ɓangaranci ba.
Ya ce kafin ya bayyana sunan Kashim Shettima, sai da ya tuntuɓi jama’a da dama, sannan kuma ya yi amfani da ta sa basirar, kamar irin yadda ya yi har ya kafa ƙasaitacciyar gwamnati a Jihar Legas lokacin da ya yi gwamna tsaron shekaru takwas, daga 1999 zuwa 2007.
Ya ce batun zaɓen 2023, tilas sai ‘yan Najeriya sun fifita nagarta kan bambancin addini da ƙabila.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa tilas fa sai ‘yan Najeriya sun zaɓi mutumin da ya fi cancanta, maimakon karkata kan addinanci da ƙabilanci a zaɓen 2023.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, a cikin bayanin da ya fitar, jim kaɗan bayan ya bayyana Bola Tinubu a matsayin mataimakin takarar sa na zaɓen shugaban ƙasa a 2023.
Duk da adawa da rashin amincewa da Tinubu ya ɗauki Musulmi matsayin mataimakin takara, Jagaban Bargu ya ɗauki tsohon Gwamnan Jihar Barno, Kashim Shettima.
Ya ce ya ɗauki Shettima ne saboda ya yi amanna cewa, “Shettima mutum ne wanda zai iya taimaka min na yi gwamnatin da ba a taɓa yin irin ta ba a Najeriya. Gwamnati wadda kowane addini zai gamsu da ita ba tare da nuna addinanci da ƙabilanci ba.”
Tinubu ya ce Najeriya fa tilas sai yi watsi da wasu sagwangwamai waɗanda su ka dabaibaye ta tsawon shekaru masu yawa, idan ana so ƙasar ta ci gaba.
“Tilas sai mun riƙa tsayawa a cikin natsuwa mu na maida hankali kan inda ƙwarewa da cancanta ta fi tasiri, fiye da batun ɓangaranci.”
Wannan jarida ta bada labarin cewa Tinubu ya zaɓi Kashim Shettima matsayin mataimakin takarar sa. Shettima dai a yanzu haka sanata ne daga Jihar Barno.
Tinubu ya ayyana sunan sa a garin Daura, lokacin da ya kai wa Shugaba Muhammadu gaisuwar Babbar Sallah.
Tinubu ya ce takarar da ya fito ta shugaban ƙasa, amsa kira ne da jama’a a faɗin ƙasar nan, waɗanda su ka nemi ya fito takara. Saboda haka zai jajirce domin lamarin wani gagarimin aikin hidimar ƙasa ne.
“Saboda haka zan kafa ƙasaitacciyar gwamnati wadda za ta ƙunshi ƙwararru daga sassa daban-daban na ƙasar nan, ba tare da yin la’akari da addini, yanki ko ƙabilar mutum ba.”
Discussion about this post