Mataimakin takarar Atiku Abubakar a PDP, Ifeanyi Okowa, ya bayyana cewa takardun sa na kammala makarantar sakandare (WASC) sun salwanta, amma fa ya samu sakamako mai kyau.
“Takardun kammala sakandare na sun salwanta, amma an buga min kwafe ɗin su daga Kwalejin Edo, inda na yi karatun sakandare, ta cikin birnin Benin, wadda ta tabbatar da cewa na samu giredin sakamako.
“Satifiket ɗi na na HSC na haɗe da takardun da na miƙa wa Hukumar Zaɓe, wanda Kwalejin Edo su ka tabbatar cewa na samu ‘A’ ‘B’ ‘AB'”, inji Okowa, Gwamnan Jihar Delta.
Okowa ya yi wannan magana ce a cikin wani jawabi da ya fitar ga Sashen Manema Labarai na Gidan Gwamnatin Jihar Delta a Asaba.
Ya yi wannan bayani a ranar Talata, yayin da ya ke magana da manema labarai, bayan ya yi duba-garin wasu ayyuka a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Delta, a Ozoro cikin Ƙaramar Hukumar Isoko ta Arewa.
“Ba yabon kai ba, amma na samu sakamako mai kyau a jarabar fita sakandare (WASC), wanda da wahala a samu irin haka a wancan lokacin.
“Saboda ni ne na zo na biyu a ƙasa baki ɗaya a lokacin, bayan mun kammala sakandare a 1976. Dalili kenan a lokacin da na kammala jami’o’i da dama su ka ɗauke ta hanyar saƙon ‘Telegram’. Ni kuma sai da na tsaya na darje na zaɓa.”Inji Okowa.
Okowa ya bayyana cewa lokacin da ya kammala Jami’ar Ibadan bai ma cika shekaru 22 ba.
Ya ce masu cewa ba shi da takardun kammala sakandare maƙaryata ne, masharranta kuma ‘yan yarfe. Su dai mutane komai sai sun jefa yarfen siyasa a ciki.” Inji Okowa.
Idan ba a manta ba, ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu ya shaida cewa an sace masa na sa takardun sakandare ɗin.
Sai dai kuma Tinubu har yau bai koma makarantun da ya ce ya kammala don ya karɓo sakamakon da ya ce sun salwanta ba.