Yayin da ‘yan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC su ka riƙa hawa ”duro’, ɗaya-bayan-ɗayan su na bayyana janye wa Bola Tinubu, a ranar 8 Ga Yuni, a Abuja, cikin daren kuma a tsakiyar taron gangamin tsayar da ɗan takara, an riƙa tura saƙonnin tes mai ɗauke da sanarwar cewa:
“A yi fatali da takarar Musulmi shugaba mataimakin sa ma Musulmi.”
Babu wanda ya san wanda ya fara tura wa masu zaɓen ‘yan takara wannan saƙo. Amma dai buƙatar tura saƙonnin na nufin a saka waswasi ga masu zaɓen ‘yan cewa idan su ka zaɓi Tinubu, wanda Musulmi ne da Kudu, zai fuskanci matsala idan ya tsayar da ɗan takarar mataimakin takara Musulmi.
Tinubu ne kaɗai a lokacin ɗan takarar shugaban ƙasa mai ƙarfi daga Kudu maso Yamma. Kuma shi ne kaɗai wanda idan ya ɗauki ɗan takara Musulmi daga Arewa zai haifar da matsala ga jam’iyya. Kenan kai-tsaye saƙon an tsara shi tare da tura wa masu zaɓe shi ne don a taɗiye Bola Tinubu ya faɗi zaɓen fidda-gwani.
An samu wani jami’i daga cikin APC ya tashi a wurin taro ya soki wannan tuggu da aka nemi ƙullawa kafin a fara jefa ƙuri’a.
Sama da wata ɗaya bayan zaɓe, Tinubu ya aikata abin da aka nemi shirya masa tuggun kayar da shi don kada ya aikata. Wato ɗaukar mataimakin takara Musulmi, Kashin Shettima. Tun daga nan kuwa jam’iyyar APC ta shiga cikin tirniƙu, wai faɗan Ibilisai yaro bai gani ba balle ya raba.
Batun Maida Mulki Kudu:
A can baya kafin lokacin fidda gwani, maganar da ake yi ita ce mulki ya koma Kudu. Ko a Kudu ɗin ma, Kungiyar Kiristoci ta Ƙasa, CAN ta ce sai dai a bai wa Kirista mulki ko a Kudu ɗin ma.
Amma kuma bayan da aka dirar wa CAN da surutun cewa ta na baƙin ciki da takarar Tinubu, Musulmi ɗan Kudu, sai CAN da sauran su duk su ka koma cewa lallai ba za su yarda da ‘Muslim-Muslim’ a APC.
Don haka ba abin mamaki ba ne da ɓangarorin Coci-coci daban-daban musamman a Arewa, su ka yi fatali da ɗaukar Shettima matsayin ɗan takarar shugaba ga Tinubu.
Ire-iren su Shugaban CAN na Kaduna, John Hayab, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal da Sanata Abbo na sahun gaban ragargazar APC da Tinubu. Baya da wasu da su ka fice daga APC saboda kishin Kiristanci.
Lawal na cikin ‘yan Kwamitin APC na fito wa Tinubu mataikakin takara. Kuma ya bayar da shawarwarin da su ka ƙunshi matsalar ɗaukar mataimakin takara Musulmi ko Kirista mataimakin takara daga Arewa.
Yayin da kwamiti ya bada shawarar cewa idan aka fidda mataimakin takara daga Arewa kuma Kirista, to za a ɗinke rashin jituwa a yankin. Amma kuma Musulmi a Arewa da maso Yamma da Arewa maso Gabas duk NNPP da PDP za su zaɓa.
Kenan Muslim-Muslim a APC ƙara wa takarar NNPP da PDP ƙarfi zai yi. Kuma dama a yankunan ne yawan ƙuri’un da za a jefa su ke.
Sannan kuma sun ce takarar Muslim-Muslim a APC zai haifar da bijirewa daga Kiristocin Arewa, wanda hakan zai jefa APC cikin asarar miliyoyin ƙuri’u.
Tun daga lokacin da aka ɗauki Kashim Shettima mataimakin takarar Atiku, ake ya yamutsa gashin baki a jaridu, radiyo, gidajen talabijin, kasuwanni, cikin motocin hawa, gidajen barasa, tashoshin mota da teburin mai shayi.
Sai Da Aka Yi Gargaɗin Wannan Guguwa Tun Kafin Ta TIrniƙe:
Shin me ya sa duk da haushin da Kiristoci ke ji cewa ba a ba su takara a Kudu ba, sai aka bai wa Tinubu Musulmi, a hakan kuma ya rufe ido ya zo Arewa ya ɗauki mataimakin takara Musulmi?
Yayin da takarar marigayi Abiola da Kingibe a 1993 waɗanda dukkan su Musulmai ne, ba ta tayar da ƙura ba sai samun goyon baya, takarar Tinubu da Shettima kuma na neman maida wa APC hannun agogo baya.
Abin dubawa shi ne yadda manyan ‘yan takara huɗu na APC, PDP, LP da NNPP daga shiyyoyi daban-daban su ka fito, ana ganin cewa kowa a cikin su akwai shiyya ko jihohi daban-daban.
Atiku na PDP a Arewa maso Gabas ya fito. Kwankwaso daga Kano, tsakiyar yankin, jihar da aka fi samun yawan ƙuri’u.
Peter Obi daga Kudu Maso Gabas, shi kuma Tinubu daga Kudu maso Yamma.
Zaɓen gwamnan Jihar Osun ya firgita APC, ganin yadda PDP ta yi mata ƙwacen goriba a hannun kuturu.
Tarangahumar Tinubu:
Tinubu ya shiga tsaka mai wuya, abin da Hausawa ke kira gaba damisa baya siyaki.
Akwai matsalar ƙalubalen siyasa, akwai na addini, akwai na ƙabilanci, akwai na siyasa, akwai na addinantar da siyasa da kuma siyasantar da addini.
Dabara dai ta rage ga mai shiga rijiya. Ko ya taka tsani ya shiga, ko kuma ya yi ƙundumbala ya zunduma a ciki.
Discussion about this post