Kungiyar Afenifere ta Yankin Yarabawa ta bayyana cewa a zaɓen 2023 Peter Obi za ta yi ba Bola Tinubu ba.
Afenifere kungiyace ta dake rajin kare hakkin Yarabawa wacce da ita ce Tinubu ya haɗa kai a 1999 ya zama gwamnan jihar Legas.
A wancan lokacin kungiyar ce ta rikiɗe ta zama jam’iyyar AD.
Bayan haka sai auratayyan dake tsakanin su ta lalace, Tinubu ya kirkiro ACN wacce Atiku Abubakar yayi takarar shugaban kasa a ciki a 2007.
Afenifere ta ce dalilin da ya sa ba zata yi wa Tinubu aiki ba shine ganin idan ya yi nasara zai cigaba da abinda Buhari ya ke yi ne yanzu.
” Tinubu zai cigaba da irin mulkin Buhari ne, mu kuma da ƴan Najeriya mun koɗu. Amma Peter Obi ya san abinda ya kamaci Najeriya, yana da kwarewa sannan kuma ya san yadda zai kulle ya kuma ɗunke barakar da ake fama da su a kasar nan.
” Bayan haka a namu ra’ayin yanzu lokaci ne da Inyamirai za su yi mulkin kasar nan. Tunda abin ya dawo yankin Kudu, ɗan ƙabilar Igbo ne ya fi dacewa ya mulki Najeriya, shine ya sa dukkan mu Yarabawa za mu dangwala wa Obi.
Wannan matsaya na Afenifere ya zo adaisai jam’iyyar APC da Tinubu na fuskantar tsananin adawa daga Kiristocin Najeriya saboda zaɓen musulmi mataimaki da yayi.
Kiristocin APC sun lashi takobin cewa lallai za su yi amfani da karfin su su kasa Tinubu savoda ya zaɓi musulmi, Kashim Shettima, mataimaki.
Discussion about this post