Yayin da saura makonni 10 jam’iyyun siyasa su fara karaɗe ƙasar nan da kamfen ɗin yaƙin neman zaɓen 2023, mutane da dama na hasashen cewa zaɓen wanda za a yi cikin watan Fabrairu 2023 ba zai bambanta da zaɓen da aka yi na Jamhuriya ta Huɗu ba.
Cibiyar Inganta Dimokraɗiyya na Ƙasa da Cibiyar Siyasar Jamhuriya ta Amurka duk su ma sun yi hasashen haka zaɓen zai kasance.
Tawagar cibiyoyin biyu dai sun kawo ziyara a Najeriya a ranakun 13 da kuma 22 Yuli, domin duba-garin irin shirye-shiryen da aka fara na zaɓen tun kafin lokacin ya ƙarato. Cibiyoyin sun ce akwai yiwuwar tafiya zagaye na biyu a zaɓen.
Cikin sanarwar da su ka raba wa manema labarai a ranar Juma’a, tawagar ta ce fitowa takarar Peter Obi da Rabi’u Kwankwaso zai iya sa a tafi zagaye na biyu na zaɓen.
“Wannan ne karo na farko da za a yi zaɓe babu shugaban da ke neman zarcewa tun 2007.
Mene Ne Zaɓe Zagaye Na Biyu?
A ƙarƙashin Dokar Najeriya ta 1999, zaɓen shugaban ƙasa, za a iya yin zagaye na biyu idan ‘yan takara biyu da ke kan gaba da sauran jam’iyyu ‘yan takarar su ba su samu aƙalla kashi 1 bisa 4 na ƙuri’un jihohi 2 bisa 3 na jihohi 36 na faɗin ƙasar nan.
Sai dai kuma duk da cukumurɗar bambance-bambancen da ke tsakanin ‘yan Najeriya, har yau ba a taɓa tafiya zaɓe zagaye na biyu ba.
Kuma tun daga 1999 har yau ba a zaɓi shugaban da ya samu ƙasa da kashi 53 na ƙudirin da aka kaɗa ba. Amma kuma zaɓen 1999 Obasanjo ya damu kashi 62.78 na yawan ƙuri’un da aka jefa, shi kuma Olu Falae na AD ya yi takara a bisa doron jam’iyyu biyu, AD da APP.
Ko Shigar Kwankwaso Da Peter Obi Zai Canja Salon Zaɓen Shugaban Ƙasa A Najeriya?:
Abin tambaya a yanzu ganin Kwankwaso da Obi su ka da ƙarfi sosai, shin ko za su iya yin tasirin da za a kai ga yin zaɓe zagaye na biyu kuwa? Ko ɗaya daga cikin su zai iya zama ƙarfen-ƙarfar da zai zame wa sauran ‘yan takarar ƙarfen-ƙafa lokacin zaɓe?
‘Yan Takarar Raina Kama Ga Gayya:
Jam’iyyun LP da NNPP duk ‘yan takarar su na nuna cewa su ke da alamomin yin nasara a zaɓen idan jam’iyyun biyu sun haɗa kai wuri ɗaya.
To amma da ya ke kowanen su ya tsaya takara shi kaɗai. Shin ko a cikin su akwai wanda zai zame wa Atiku da Tinubu ƙarfen kafa?
Kwankwaso Ɗin Ne Ko Peter Obi?:
Yayin da aka ɓata wa Obi rai a PDP ya koma LP, sunan Peter Obi ya karaɗe ƙasar nan da duniya a shafukan soshiyal midiya, musamman Tiwita.
Sai dai kuma babu wani tauraro a cikin LP baya ga shi Peter ɗin. Haka kuma jam’iyyar ta kasa yin cara a wasu jihohi idan banda yankin Kudu maso Gabas, inda Obi ya fito, wato yankin ƙabilar Igbo.
Shi kuwa Kwankwaso tun bayan tsayawar sa takara jam’iyyar ta sa ke ƙara samun tagomashi, inda manyan hasalallun ‘yan PDP da na APC da zaɓukan fidda gwani bai yi masu daɗi ba. Su ne su ka riƙa tururuwa cikin jam’iyyar, musamman a dukkan jihohin ƙasar nan.
Kwankwaso ya ja zugar tsoffin gwamna, Sanatoci da Mambobin Tarayya da ke kan mulki da kuma tsoffin su da kuma miliyoyin magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya.
Yayin da Obi ya ɗauki Datti Baba-Ahmed mataimakin takarar sa daga jihar Kaduna, har yanzu Obi bai samu karɓuwa sosai a Arewa ba. Saboda haka ya na buƙatar samun karɓuwa a Arewa.
Duk da Kwankwaso ya samu karɓuwa a Arewa, kuma ya ɗauko Rabaran Idahosa daga Jihar Edo a matsayin mataimakin takarar sa, wanda kuma mazaunin Legas, akwai aiki a gaban Kwankwaso na ƙara yayata jam’iyyar a lunguna da saƙonnin sauran sassan ƙasar nan.
Atiku Abubakar Da Tinubu:
Tsoffin abokai biyu sun kasance ‘yan takara biyu na gaba, ko don saboda kasancewar su suna wakiltar manyan jam’iyyu biyu.
PDP ta yi mulki shekaru 16 da wata bakwai. Su biyun sun kasance jihohi 35 na hannun su, kuma yawancin ‘yan majalisar tarayya da Sanatoci duk na su ne. Sun kuma gina ɗimbin masoya. Sannan kuma sun fi ƙwarewa wajen fifikon tara magoya baya da iya tara maƙufan kuɗaɗen takara.
Haka APC da PDP duk su na da nauyin aljihu da ke cike da kuɗi, har su na rangaji.
Duk da APC da PDP sun nuna ƙarfin su a zaɓen Ekiti da Osun kwanan nan, LP da NNPP ba su nuna wani kataɓus a zaɓukan ba.
APC da PDP na fama da kurwar da ta kama su, kuma ta ƙi saki har ranar yin zaɓe.
Yayin da Atiku ya samu matsala wajen fitar da Ifeanyi Okowa ɗan takarar sa na mataimaki, maimakon Nyesom Wike, shi kuwa Tinubu takarar tikitin Muslim-Muslim, bayan ya ɗauki Kashim Shettima matsayin ɗan takarar mataimakin shugaba.
Discussion about this post