Na baya-bayan nan shi ne Sabon Sarkin ‘Yandoton Daji, Aliyu Marafa, wanda aka dakatar a ranar Lahadi, saboda naɗin da ya yi wa ɗan ta’adda Ada Aleru, wanda aka ba sarautar gargajiya ta Sarkin Fulanin ‘Yandoton Daji, a ranar Asabar.
Gwamna Bello Matawalle ne ya ƙirƙiro masarautar ‘Yandoton Daji daga cikin Ƙaramar Hukumar Tsafe, a ranar 18 Ga Mayu.
Wannan sabuwar masarauta ta ƙunshi ‘Yandoton Daji, Keta, Kizara, Bawa Kwanga, Kwaren Ganuwa, Ɗanjibga da Ƙuncin Kalgo. Hedikwata kuma a ‘Yandoto.
Sai dai kuma ba Marafa ba ne basaraken da aka fara tsigewa ko dakatarwa saboda zargin kusanci da ‘yan bindiga ba.
Tun daga 2019 Gwamna Matawalle ke yawan zargin masu riƙe da sarautun gargajiya da laifin haɗa baki da ‘yan bindiga masu kai hare-hare a wasu garuruwa daban-daban. Hakan ta kai Matawalle tsige wasu da kuma dakatar da wasu sarakunan gargajiyar.
Sai dai kuma shi ma Matawalle, har yau bai taba sa an caji waɗanda ake zargin a kotu ba.
Sarkin Maru:
Gwamna Matawalle ya tsige Sarkin Maru, Abubakar Cika a cikin watan Agusta, 2019, saboda goyon bayan ‘yan bindiga. Dama tun cikin Yuni aka dakatar da shi, bayan da ‘yan yankin masarautar sa sun yi zangin shi da barayin shanu.
Sarkin Zurmi:
Cikin watan Yuni, 2021 aka dakatar da Sarkin Zurmi Atiku Abubakar saboda alaƙa da ‘yan bindiga.
An dakatar da shi bayan ‘yan bindiga sun kai hari sun kashe mutum 61 a lokacin da su ka kai harin.
Sarkin Ɗansadau:
Gwamna Matawalle ya dakatar da Sarkin Ɗansadau, Husaini Umar, saboda alaƙa da Boko Haram.
Sauran sarakunan gargajiya da aka kora ko aka dakatar, sun haɗa da Hakimin Kanoma Lawali Ahmed, a cikin 2019, tare da Sarki Abubakar Chika.
Akwai kuma Hakiman Kanwa, Ɓurmi, Garba Kanwa, Ɓurmi da Bello Yusuf daga Zurmi.
Discussion about this post