Sau da yawa mutane sukan rika ɗaukar wasu abubuwa da suka saba yin su a kullum ya zama abu na dole gwamnati ko ko wasu mutane ba su da damar cewa komai akai koda ko ya kasance abu ne wanda ke karkashin iko na gwamnati.
Addinin musulunci ba da ka ake yin sa ba, ko ina aka kafa doka ko shari’a akan abu dole mutane su bi kuma su amince da shi muddun bai saɓa wa dokar Allah ba da karantarwar Annabi Muhammadu SAW.
Maganar cewa wai gwamnati ta saka dokar sai an biya kuɗi kafin a yi sallar Idi a filin Murtala Square bai saba wa addini ba domin filin ba an gina shi don yin sallar Idi bane. Ko da yake an ce gwamnati ta janye hakan yanzu, amma ko yanzu ko a gaba masu yin sallah su nemi wuri domin gwamnati ta na da iko da damar yin avinda ta ga ya dace wa jihar tunda ba filin dama an gina shi don haka bane.
Ko da ko ace wai magaba da dama sun yi sallar Idi a wannan fili bai zama dole ba idan kuma aka damu canji na yanayi da lokaci hakan ya canja domin shi kan shi rayuwa ma canja wa ya ke yi.
Murtala square fili ne na gwamnati tun farko sannan kuma fili ne na gudanar da taruka da wasanni. Wannan gwamnati ta Kaduna ƙarkashin Nasir El-Rufai ta gina shi, ta ƙayata shi ta maida shi abin alfahari ga ƴan Kaduna da duk wani bako da ya ziyarci jihar. Sannan kuma ta ce tunda wuri ne na wasanni da sauran su za a guara shi fomin hala kuma za a maida shi wuri da duk abinda za a yi wanda bai shafi abinda aka tanade shi don ati ba toh sai dai a biya.
A ganina banga illar haka. Sai masu sallah su nemi wani filin su rika yin sallar su tunda dama ba siyan wurin suka yi ba gwamnati ce ta badu ikon yin haka.
Ko mu jima ko mu dade wata rana za a daina sallar Idi a wurin don ba a gina a matsayin masallacin idi ba. Banga dalilin da wasu za su saka siyasa a ciki ba. Duk da cewa ni ba ɗan asalin jihar Kaduna bane, ban taɓa tunanin akwai gwamnatin da zata iya yin ayyukan da gwamna Nasir El-Rufai ya yi a jihar ba. Kuma dama iata ci gaba idan an son shi sai dole an yi abinda ya dace.
Idan ba a hana sallah yanzu ba, to za ahana yin sallah a wannan wuri wata rana ko da kuɗi ko ba kuɗi saboda haka masu yin sallah a wururin su kwana da shirin hakan zai faru, su nemi wani wurin sallar Idi.
Discussion about this post