Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta bayyana Ademola Adeleke na PDP cewa ya yi nasara a zaɓen gwamnan Jihar Osun.
Da ya ke sanarwar a safiyar Lahadi, Baturen Zaɓe na Jihar Osun Oluwatoyin Ogundipe, ya bayyana cewa, “Ademola Adeleke na PDP ya samu ƙuri’u 403, 371. Shi kuma Gwamna Gboyega Oyinlola ya samu 375, 027.”
“Saboda ka samu yawan waɗannan ƙuri’u, to ka cika sharuɗɗan cin zaɓe. Don haka kai ne ka yi nasarar zaɓen gwamnan jihar Osun, wanda aka yi ranar Asabar, 16 Ga Yuli, 2018.
Baya ga lashe zaɓen, Adeleke ya yi nasara a Ƙananan Hukumomi 17 daga cikin 30 da ke jihar.
Mutane da dama na ganin wannan zaɓen nuniya ce ga jam’iyyar APC cewa fa an gaji da ita kuma a shirye ake a bata wuta a zaɓe mai zuwa.
Idan ba a manta ba, Buhari ne kawai bai tafi garin Osogbo ba domin yin kamfen. Baya ga gwamnoni, shi kansa ɗan takarar shugaban Kasa na APC Bola Tinubu ya halarci gangamin jam’iyyar amma bata haifar musu da ɗa mai ido ba.
Tun daga farko dai ƴan jihar da matasa da suka fito zaɓe suka fara bukin damun nasara a zaɓen kafin a kammala bayyana sakamakon zaɓe.
Jihar Osun na da matukar muhimmanci ga Yarabawa domin tana daga cikin manyan jihohin dake da masu ƙuri’u masu yawa a yankin Kudu Maso Yamma.
Discussion about this post