Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya ragargaji ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, jam’iyyar sa Atiku Abubakar cewa makaryaci ne.
” Kwanannan zan fara to in fayyace komai kowa ya san ainihin abinda ya faru da kuma abin da ake ciki, da kuma yadda wasu jigajigan PDP waɗanda karnukan farautan Atiku ne suke yi mini bita da ƙulli.
” Kafin Atiku ya zaɓi mataimakin sa, Okowa, ya san hanyar gida na, ya na zuwa. Amma yanzu bai san hanyar ba. Sai ana cewa wai ya tura wasu su ganni. Yanzu ne zai tura wasu. Ya manta hanyar gida na ko?
Wike ya ce ya dawo Najeriya daga hutu domin ya cigaba da aikin sa a matsayin gwamnan jihar Ribas. ” Da zaran na kammala kaddamar da ayyukan da za mu kaddamar a jihar Ribas, zan bi su ɗaya bayan ɗaya in ba su amsa. Duka karnukan farautar Atiku su saurare ni, zan ba kowane dayan su amsa daidai da irin maganar da yayi akai na ko kuma korafinsa.
Idan ba a manta ba tun bayan zaɓar Ifeanyi Okowa da Atiku yayi, jam’iyyar PDP ta tsage gida biyu, wasu daga cikin jigajigan jam’iyyar suka karkata zuwa ɓangaren Wike, wasu kuma ɓangaren Atiku.
Dukkannin su ba su ga maciji da juna, hakan yasa kowa ya ja daga.
Discussion about this post