A yanzu dai ko yaro na goye a ƙasar nan ya kwana da sanin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar na cikin gagarimar matsalar da za a iya cewa ya janyo wa kan sa, tun bayan da ya yi gaban-gabarar watsi da shawarwarin manyan jam’iyya, ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Kusan gaba ɗayan manyan ƙusoshin jam’iyyar PDP sun cika da mamakin yadda Atiku ya yi watsi da shawarar da kwamitin fidda mataimakin shugaban ƙasa ya ba shi, cewa Gwamna Nyesom Wike ne na Jihar Ribas ya fi dacewa da kuma cancanta Atiku ya ɗauka takarar mataimaki.
Atiku ya hamɓare kwandon shawarar da aka ba shi, bayan da ya yi masu alwashin cewa zai yi aiki da shawarar ta su, ya ɗauki Okowa, ba tare da tuntuɓar su, ko sanar da su dalili ba.
Raddin Gwamna Ortom Kan Atiku: Ba Ni Ta Tababcin Zan Goyi Bayan Atiku A Zaɓen 2023:
Shugaban kwamitin mutum 17 da PDP ta kafa domin fitar wa Atiku Abubakar ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, wato Samuel Ortom na Jihar Benuwai, ya fusata da yadda Atiku ya yi watsi da shawarar da su ka ba shi, inda ya ɗauki Ifeanyi Okowa a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, maimakon Gwamna Nyesom Wike da su ka rattaba, su ka miƙa masa sunan sa.
Cikin wata tattaunawa da ARISE TV ta yi da Ortom a wannan makon, ya ce Atiku ya baɗa masu ƙasa a ido, ya yi watsi da matsayar da su ka ɗauka.
Wani ƙarin haushi a cewar Ortom shi ne yadda Atiku har yau bai tuntuɓi Wike ya ba shi haƙuri ba, kuma Atiku bai shaida wa kwamiti dalilin sa na ƙin ɗaukar Wike ba.
A kan haka ne Ortom ya ce shi fa a yanzu dai haƙiƙa ya dawo daga rakiyar Atiku, hankalin sa bai kwanta cewa zai goyi bayan zaɓen sa a 2023.
“Ba na jin zan goyi bayan takarar Atiku, amma dai zan ci gaba da yin addu’a idan Ubangiji na ya ƙaddare ni da mara wa Atiku baya, to shikenan sai na yi haka ɗin. Amma dai har yanzu kam ya fita daga harkokin gaba na.”
Ɗan Kudu Mu Ke So A Ba Takara, Ba Atiku Ba -Ayo Fayose:
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya fito ƙarara ya ce Atiku ya ci amanar Wike, don haka ba zai goyi bayan kamfen ɗin sa ba.
Wata gagarimar rigima ta kunno kai a cikin Jam’iyyar PDP, inda tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose ya bayyana cewa Gwamna Nyesom Wike na Rivers da magoya bayan sa kakaf ba za su goya wa Atiku Abubakar baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba.
A cikin wata tattaunawar musamman da Fayose ya yi da PREMIUM TIMES, Fayose ya ƙara jaddada cewa tabbas Atiku ya ci amanar Wike, don haka Wike da jama’ar sa za su zuba wa Atiku Ido, “tunda ya na ganin cewa shi kaɗai zai iya cin zaɓe, sai ya je ya ci ɗin.”
Fayose ya ce, “bayan Atiku ya yi nasara a zaɓen fidda-gwani, ya je har gida ya nemi haɗin kan Gwamna Wike, kuma ya yi masa alƙawarin zai naɗa shi ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
“Kuma da aka kafa kwamitin tuntuɓa wanda zai fito wa Atiku da ɗan takarar mataimaki, kwamitin ya bayar da sunan Wike.
“Amma da aka shiga aka fita, sai Atiku ya wancakalar da Wike, ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta.
“Atiku bai yi wa Wike mutunci ba. Domin bayan ya ci amanar sa ya ƙi ɗaukar sa mataimaki, ai ya-kamata ya kira Wike ya sanar da shi dalilin da ya sa ya karya alƙawarin da ya yi, wato ya ba shi haƙuri, amma Atiku bai yi hakan ba.”
Fayose ya ce har yau ya na na nan kan ra’ayin sa cewa kudu ya kamata ya yi mulki ya koma kudu a 2023.
“Yan Arewa na ganin Goodluck Jonathan bai kamata ya ci zangon ‘Yar’Adua daga 2015 zuwa 2019 ba. Saboda haka sai su ka kori Jonathan ta hanyar zaɓen Buhari a ƙarƙashin APC.
“To tunda Buhari ya kammala shekarun sa takwas, ya kamata a yi adalci a bai wa ɗan kudu mulki, ba wai a ce Atiku ne daga Arewa zai fito neman zama shugaban ƙasa ba.
“Ni ina da tabbacin cewa ko kamfen Wike ba zai taya Atiku ba. Mu da ke goyon bayan Wike, duk wanda ya ce mu zaɓa shi za mu zaɓa, amma ba zai taɓa cewa mu zaɓi Atiku ba.”
PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran Atiku, mai suna Paul Ibe. Ya ce ya kamata a daina gunguni da ƙulafuci, a haɗa kai a yi nasara, a kori APC.
Zafin Dukan Da Gudumar Da Obasanjo Ya Yi Wa Atiku Bai Daina Yi Masa Raɗaɗi Ba:
CIkin makon jiya ne tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa a rayuwar sa ya tafka manyan kura-kurai biyu.
Ɗaya daga cikin manyan kura-kurai biyu da ya ce ya yi a rayuwar sa, shi ne ɗaukar da ya yi wa Atiku Abubakar a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a lokacin takarar zaɓen 1999.
Wannan kalami tabbas bai yi wa Atiku daɗi ba, wanda a yanzu haka ya lula Dubai ya bukaguro a can.
Kaushin wannan kalamin ne ya sa Shugaban Dattawan PDP Walid Jubrin ya bai wa Obasanjo sa’o’i 48 cewa ko dai ya janye kalaman da ya yi kan Atiku, ko kuma Jubril ɗin shi ma ya fallasa Obasanjo, duniya ta ji wani mummunan aibi kan sa.
Har ila yau Atiku na shan suka kan zarge-zargen baya da aka sha yi masa musamman wajen wai da hannun sa a afkuwar wasu manyan matsalolin ƙasar nan, musamman sayar da wasu kamfanonin gwamnatin tarayya a lokacin da ya na mataimakin shugaban ƙasa.
Sannan kuma duk da rashin farin jinin da APC ke fama da shi a yanzu bayan ta shafe shekaru bakwai kan mulki, tare da kasa magance matsalolin ƙasar nan, ba a daina yi wa PDP kallon musabbabin haddasa matsalolin a shekaru 16 ɗin da ta yi ta na mulki tsakanin 1999 zuwa 2015 ba.
A wani sharhi da PREMIUM TIMES Hausa ta yi kan Atiku watanni uku kafin tsaida shi takarar shugaban ƙasa, ta yi nazarin shin:
Ko Atiku zai iya cin bugun ‘fenaretin sa’ na ƙarshe a 2023?
Cikin sharhin, an yi nazarin cewa daga cikin masu azarɓaɓi, gaggawa da zaramboton saurin fitowa takarar zaɓen 2023, wanda saura watanni 12 daidai a kaɗa ƙuri’a, Atiku ne ya fi saura yawan jaraba sa’a, kuma ya sha ganin samu ya ga rashin nasara a zaɓuka daban-daban.
Atiku Jonathan ya kayar zaɓen fidda-gwanin 2011. A zaɓen 2015 Atiku ya taimaka wa Shugaba Buhari ya ci zaɓe, sannan kuma a 2019 ya gwabza tare da Buhari, amma bai yi nasara ba.
Babbar matsalar da Atiku zai iya fuskanta ita ce rashin tantagaryar masu kishin jefa masa ƙuri’a. Amma don jama’a, Atiku ya na da jama’a. Kawai dai jama’ar da za su iya yi masa ruwan ƙuri’u ne ba shi da su.
Wannan matsalar kuwa ta fito fili ne a zaɓen 2019, musamman inda a Kano inda aka yi tunanin zai iya samun ƙuri’u kusan miliyan biyu, sai ya tashi da yawan waɗanda ba su ma kai adadin da ya samu a wasu ƙananan jihohi ba.
Atiku na samun tangarɗa a kamfen ɗin sa, ta hanyoyi da dama. Kaɗan daga cikin su akwai bada fifiko ko maida hankali kan yankin kudu wajen al’amurran masu tafiyar da kamfen ɗin sa. Ko a wannan shekarar Wazirin Adamawa ya ɗora ɗan kudu, Remond Dokpesi mai gidan talbijin na AIT a matsayin Daraktan Kamfen.
Mutane da dama na ganin kamata ya yi Atiku ya fito kawai gaba-gaɗi ya yi daraktocin kamfen biyu, wato ɗaya kudu, ɗayan kuma a Arewa.
Atiku na da matsala a siyasar rama bugun yarfen siyasa a Arewa. Hakan ya faru a zaɓen 2023, inda a Arewa aka riƙa aibata shi da yi masa yarfen siyasa daban-daban, amma babu zaratan sojojin baka a soshiyal midiya da za su riƙa rama masa sharri, yarfe da jagaliyanci da buyagin da aka riƙa yi masa.
Don sai da ta kai har a wurin zaɓe a ranar zaɓe ana bin sa da yarfen cewa “kada a zaɓi wanda ya ce zai sayar da NNPC.”
Tun daga ranar da Atiku ya ce zai sayar da NNPC a lokacin kamfen ɗin 2019, shi bai fito ya yi wa talakawa bayani dalla-dalla abin da ake nufi da sayar da NNPC ba. Sannan kuma dakarun kamfen ɗin sa da sojojin bakan sa ba su yi yaƙin wayar wa talakawan Arewa kai dangane da abin da ake nufi da ‘sayar da NNPC ba.’
Wannan ya bada wawakeken giɓin da masu adawa da shi su ka yi amfani su na yi masa yarfe, ana fassara shi da cewa mutanen sa zai sayarwa, sannan ya kewaya ya saye daga hannun su.
Wata matsala da Atiku ke fuskanta ita ce wasu da ke kewaye da shi ba ka ganin su a jikin sa sai kakar siyasa ta zo. Za su kewaye shi su hana mashawarta na ƙwarai su matsa ballantana su ba shi shawara ta gari.
Sannan akwai ‘yan ‘idan ta yi ruwa rijiya, idan ba ta yi ba masai’, masu ƙoƙarin samun na watsawa aljihu a duk lokacin da tafiyar kamfen ɗin Atiku ta kunno kai. Wasu na ƙoƙarin azurta kan su ta hanyar kamfen ɗin, ta yadda ko an faɗi zaɓe, to ba ta ɓare da su ba.
A zaɓen 2019 matasa da dama a Arewa musamman ‘yan soshiyal midiya masu kare shi, sun watsar ganin yadda ya fi mayar da hankali kan murna da samun wani matsashin soshiyal midiya daga Kano, wanda ya canja sheƙa ya koma ɓangaren sa. Sai dai kuma matashin ya gwasale Atiku, domin bai jima tare da shi ba, ya sake komawa cikin gonar da ya fito.
Wasu da dama na cewa Atiku bai fitar da kuɗi a kamfen ɗin sa na 2019 ba, kamar yadda aka yi tsammanin zai yi. To ko ma dai me kenan, wannan ce damar Atiku ta ƙarshe, matsawar shi PDP ta tsayar a matsayin ɗan takarar su a 2023.
Akwai jan aiki ga jagororin tafiyar Atiku, ko da kuwa shi ɗin ne PDP ta tsayar. A Arewa inda a nan ne aka fi samun ƙuri’un da ke kai ɗan takara ko jam’iyya cin zaɓe, siyasar ta sauya tun daga 2011, inda a yanzu addini da malaman addini na da tasiri kan masu jefa ƙuri’a. Yanzun nan sai a hau mimbari a yi biji-biji da ɗan takara, ko da kuwa babu wata ƙwaƙƙwarar hujjar yin hakan.
Malamai da dama sun fito fili su na nuna ga ɗan takarar da su ke so. Don haka akwai jan aiki ga jiga-jigan kamfen ɗin Atiku domin sanin makamar yadda za su tunkari yarfen siyasa da watsa ji-ta-ji-tar da akan yi a Arewa, kan ɗan takarar da ba shi wasu gungun ba’arin masu faɗa-a-ji ke so ya yi nasara ba.
Wannan jan aiki kuwa a gaskiyar magana, ya fi ƙarfin Dokpesi, Babban Daraktan Kamfen ɗin Atiku. Domin mutumin da tun tafiya ba ta yi nisa ba ya ke iƙirarin zai iya tuɓewa zigidir a bainar jama’a, maganar gaskiya ba irin sa ne zai ciwo wa ɗan takarar dandazon dubun-bubatar ƙuri’un matan auren Arewa ba ne. Ko dai Waziri ya tashi tsaye ya sauya takalmin bugun fenaritin sa na ƙarshe, ko kuma ya ɗinke inda takalmin ya yage tun kafin alƙalin wasa ya ba shi umarnin buga ƙwallon a 2023.
Discussion about this post