Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta bayyana Ademola Adeleke na PDP cewa ya yi nasara a zaɓen gwamnan Jihar Osun.
Da ya ke sanarwar a safiyar Lahadi, Baturen Zaɓe na Jihar Osun Oluwatoyin Ogundipe, ya bayyana cewa, “Ademola Adeleke na PDP ya samu ƙuri’u 403, 371. Shi kuma Gwamna Gboyega Oyinlola ya samu 375, 027.”
“Saboda ka samu yawan waɗannan ƙuri’u, to ka cika sharuɗɗan cin zaɓe. Don haka kai ne ka yi nasarar zaɓen gwamnan jihar Osun, wanda aka yi ranar Asabar, 16 Ga Yuli, 2018.
Baya ga lashe zaɓen, Adeleke ya yi nasara a Ƙananan Hukumomi 17 daga cikin 30 da ke jihar. APC ta samu ƙananan hukumomi 13.
Sauran jam’iyyu 13 kuwa babu wadda ta samu ko ƙaramar hukuma ɗaya.
Ramuwar Gayyar Kwankwatsar Da Su Tinubu Su Ka Yi Wa Adeleke A 2018:
Zaɓen gwamnan Osun rayuwar gayya ce Adeleke ya yi kan Oyetola, Tinubu da Shugaba Muhammadu Buhari, da kuma APC kacokan.
A zaɓen 2018, APC ta cika Osun da gwamnoni da jiga-jigai, inda aka kayar da Adeleke na PDP, bayan an yi zaɓen ‘inkwankilusib’.
An yi wa Adeleke taron dangi, inda har aka haɗa da wasu jam’iyyu, domin a kayar da Adeleke a wata rumfar zaɓe ɗaya tal.
Zaɓen yanzu na 2022 kuwa alama ce mai nuna cewa ɗan takarar APC a zaɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai sha wahala a yankin sa na Kudu maso Yamma. Tunanin da ake yi cewa zai kwashi miliyoyin ƙuri’u a ɓagas, zaɓen Osun ya nuna ba haka siyasar za ta kasance ba.
Mulkin Adeleke zai fara ne daga watan Nuwamba, sadda wa’adin gwamnan da ya sha kaye zai ƙare.
Zaɓen ya ƙara zama tarihin da ɗan takara ya kayar da gwamna wanda ke kan mulki, kuma wanda jam’iyyar sa APC ke mulki a ƙasa.
Discussion about this post