Shugaban karamar hukumar Wase a jihar Filato Ado Buba ya bayyana cewa gwamnatin sa zata siyo bindigogi domin raba wa kungiyoyin sa kai na karamar hukumar.
Buba ya ce zuwa yanzu ƙaramar hukumar ta siyo kuma ta raba wa kungiyoyin sa bindigogi kirar ‘pump action’ 80 a karamar hukumar.
Ya ce karamar hukumar na kokarin karo bindigogi domin kare rayuka da dukiyoyin mutane a karamar hukumar amma rashin kudi ya hana haka.
Buba ya ce gwamnatin sa ta siyo wadannan bindigogi ne ganin yadda rashi tsaro ya zama ruwan dare a karamar hukumar Wase.
Ya ce a dalilin rashin tsaro manoma da dama a karamar hukumar sa sun ƙasa zuwa gona a shekarar bara.
Buba ya ce samar da bindigogi wa kungiyar ‘yan sa kai zai taimaka wajen ganin bana manoma sun koma gona.
Discussion about this post