WHO ta ayyana cewa cutar Monkey Pox ta zama annoba a duniya.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar cewa cutar kurarraji Biri da ake kira Monkey pox ta za annoba a duniya.
Shugaban kungiyar Tedros Ghebreyesus ya sanar da haka ranar Asabar duk da cewa kwamitin da WHO ta kafa domin dakile yaduwar cutar ta yanke shawarar cewa yaduwar cutar bai kai matsayin da zai zama annoba ba.
A ranar 26 ga Yuni 2022 adadin yawan mutanen dake dauke da cutar ya kai 3,040 a kasashe 47.
Duk da haka kwamitin dakile yaduwar cutar ta duniya ta ce cutar bai kai matsayin annoba ba.
Zuwa yanzu cutar ta yadu zuwa kasashen 75 a cikin ‘yan makonni inda hakan ya sa cutar ta zama annoba.
Ghebreyesus ya ce ya fitar da sanarwan ne domin yin haka zai taimaka wajen daukan matakan da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar.
“Mun gano cewa cutar na yaduwa zuwa kasashen da basu da tarihin bullowar cutar ko kuma suna da alaka da kasashen da cutar ta bullo.
“Cutar ta fi yaduwa a tsakanin mazajen dake yin jima’i da ‘yan uwan su maza musamman wadanda ke da aboka saduwan da yawa.
“A dalilin haka ya sa muka sanar cewa cutar ya zama domin kasashen duniya su mike wajen daukan matakan dakile yaduwar cutar da gaggawa.
Yaduwar cutar Monkey pox
WHO ta ce wannan shine karon farko da cutar ke bullowa a kasashen da basu da alaka da kasashen dake fama da cutar.
Daga ranar daya ga Janairu zuwa 4 ga Yuni yankin kasashen Turai ne ke kan gaba a jerin yankin duniya dake fama da cutar.
Daga nan sai yankin Amurka, yankin Afirka, yankin yammacin Pacific da yankin Gabashin Bahar Rum.
Mutum 2,200 ne suka kamu da cutar a kasar UK daga cikin duban da suka kamu a duniya.
A ranar Juma’a kasar Amurka ta sanar cewa ta gano cutar a jikin Yara kanana.
Hukumar dakile yaduwar cututtuka na kasan CDC ta ce wannan shine karon farko da suke gano cutar a jikin yara kanana.
Menene cutar Monkey pox
Cutar ‘Monkey Pox’ cuta ce da take kama fatar mutum inda zaka ga mai dauke da cutar na fama da wasu irin manya-manyan kuraje kamar kazuwa.
Cutar ya fara bullowa a Nahiyar Afrika a shekarar 1970 sannan ya bayyana a shekaran 1978 a Najeriya.
Tun daga wancan lokaci cutar bata sake bayyana ba sai a shekarar 2017 a jihar Bayelsa.
Yadda Monkey Pox ke shiga cikin jikin dan Adam
Rahotanni sun nuna cewa namun daji kamar su birai da beraye dake shawagi a gidajen mutane na daga cikin ababen dake kawo cutar ‘Monkey Pox’.
Sannan kuma cutar na yaduwa idan ana yawan zama kusa da wadanda suka kamu da cutar.
Ana kuma iya kamuwa da cutar idan aka yi jima’i da wanda ya ke ɗauke da cutar.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce kwayar cutar ‘Monkey Pox’ yakan dauki tsawon kwanaki 6 zuwa 16 kafin ya fara nunawa a jikin mutum.
Alamun dake nuna an kamu da cutar monkey pox
1. Zazzabi.
2. Yawan jin gajiya a jiki.
3. Ciwon jiki musamman baya.
5. Kumburin jiki musamman idan cutar ta fara nunawa.
6. Bayyanan kuraje a jiki
Hanyoyin da za a bi don gujewa kamuwa daga cutar
1. A daina cin naman dabbobin daji kamar su biri, burgu da bera.
2. A hana dabbobi yawo musamman wadanda ke kiwon su domin kada su fita su dauko cutar daga jikin dabbobin da suke dauke da cutar kuma a killace dabbobin da suka kamu da cutar saboda hana yaduwar ta.
3. Mutane su nisanta kansu daga dabbobi musamman daga kashin su da kuma jikinsu.
4. Kada a zauna daki daya da mutanen da suka kamu da cutar.
5. A yi amfani da safan hannu wajen kula da mutanen da suka kamu da cutar musamman ma’aikatan asibiti sannan idan aka ziyarci wanda ke dauke da cutar a tabbatar an wanke hannaye da ruwa da sabulu bayan an fito.
6. A tabbatar cewa a kowani lokaci ana tsaftace muhalli.
7. Sumbatar mai dauke da cutar kan iya sa a kamu.
8. A rage shan hannu ko ta yaya sannan a yi amfani da man tsaftace hannu.
9. Hukumar dakile yaduwar cututtuka dake kasar Amurka CDC ta ce Kaurace wa juna, mutum zai iya yi wa kansa wasa har sai ya samu gamsuwa da rufe bangaren jikin da kurarrajin cutar suka feso kafin a sadu.
Discussion about this post