Maganar harkar tsaro wani abu ne da a gaskiya ban cika son yin magana akansa ba, saboda mutanenmu basa fahimtar al’amura ko son zuciya ya yi musu katutu.
Ko mun ƙi ko mun so muna da yaƙini Al-Ummarmu ta daɗe da fara lalacewa, saboda son abin duniya. Rashin aminci da amana sun yi yawa a cikinmu. Sata da ha’inci sun zama al’ada a cikinmu, ɗan kuskure kaɗan mutum zai yi ya rasa abin mallakarsa ko a damfare shi. Wannan musiba har wuraren Ibadah da maƙabartu ba su tsira daga sharrinsu ba. Babu matsala mafi girma a rayuwarmu fiye da rashin nagartan halayenmu da ɗab’iunmu.
Ɗauko harkar tsaron, mutanenmu sun ɗauka Gwamnati da ƙarfin tuwo ne za ta kawo tsaro, babu gudunmawar Al-Ummah a ciki. Da can da ake zaune lafiya da ƙarfin Gwamnati ya samu? Da can mutanen kirki sun fi yawa sai aminci da amana suka wanzu a bayan ƙasa, yanzu kuma mutanen banza sun fi yawa dole rashin aminci da tsaro su addabe mu.
Wani zai baka misali da wata ko wasu ƙasashe ya ce maka ai gwamnatocin ƙasashen basa wasa da harkar tsaro, amma ya kasa bambancewa halaye da ɗab’iun waɗancan kasashen ba irin namu ba ne. An wari gari mafi yawan masu shiga harkar tsaro suna da gurɓatattun ɗab’iun da halaye, za su iya yin komai matuƙar za su samu kuɗi mai yawa. To, ta ya ya za mu zauna lafiya?
Idan babu aminci da amana a tsakanin masu zama a cikin birane da ƙauyuka dake da karatun Addini, Boko da wayewar rayuwa ta yadda kowa ke kaffa-kaffa da komai nasa, ya muninsa zai kasance ga masu zama a daji babu Arabi babu Boko? Idan mutum ya yi mamakin rashin tausayinsu da rashin sanin ya kamatansu da gangar yake yi.
Maganganun gaskiya suna da yawa, saboda haka, kowa ya zauna ya yi nazari domin duk yadda ake tsammanin wannan matsalar ta wuce nan. Ba maganar zamanin mulkin wane ba ne, maganar halayenmu gyaruwa su ke yi ko ƙara lalacewa su ke yi.
Gurɓatattu sun yi yawa a cikin harkar tsaro, siyasa da ɗaiɗaikon Al-Ummah. Akwai masu ruruta harkar rashin tsaro saboda kuɗi daga cikin jami’an tsaro, sai masu yi saboda siyasa a matsayin camfen, wanda shi ma haɗari ne babba, sai wasu a cikin Al-Ummah da suka mayar da harkar hanyar samun kuɗi; kodai a matsayin masu bada bayanan sirri (informants) ko masu kai ma ƴan bindigar kayan masarufi.
MAFITA:
Dole sai Al-Ummah ta tashi tsaye wajen gyara halaye da ɗab’iun mutane idan fa ana so aminci ya dawo wannan ƙasar. Domin da jami’an tsaro da ƴan siyasa daga cikin Al-Ummah ake ciro su. Mafi yawan ƴan Najeriya dake ihun a gyara Najeriya, za ta gyaru cikin sauƙi idan sun gyara halayensu. Allah Ya taimake mu wajen gyara halayenmu da taimakawa Al-Ummah gaba ɗaya ta gyaru, ameen.
MMD: Abu Yahya (Aslam)
Discussion about this post