Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta na shirin haramta haya da baburan acaɓa da amfani da kowani irin babur don amfanin kai a faɗin ƙasar nan, domin ƙoƙarin daƙile matsalar tsaro.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan tashi daga taron Majalisar Tsaro ta Ƙasa, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Alhamis, a Abuja.
Malami ya ce an fahimci ana shigar wa ‘yan ta’adda da muggan makamai a maɓuyar su ne ta hanyar amfani da babura, shi ya sa za a hana amfani da su kwata-kwata a ƙasar nan.
Malami ya ce ya zama wajibi ‘yan ƙasa su sadaukar da wata hanyar sauƙaƙe rayuwar su, matsawar dai yin hakan zai iya magance matsalar tsaron da ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa.
Sai dai ya ce sai an daure sosai, domin ya zama tilas gwamnati ta ɗauki matakin domin a ci moriyar tsaron da za a samar a faɗin ƙasar nan.
Malami ya ce kuma za a haramta haƙar ma’adinai a dukkan dazukan fadin ƙasar nan, domin kawar da dandazon ‘yan bindigar da ke cikin dazukan.
Da ya ke magana kan waɗanda za su tagayyara idan aka haramta amfani da baburan haya, Malami ya ce an yi nazari cewa gaba ɗaya masu amfani da baburan haya a Najeriya ba su wuce kashi 20 daga cikin mutane miliyan 206 na adadin ‘yan Najeriya ba.
Idan ba a manta ba, kwanan baya ‘yan bindiga sun kashe sojoji 30 a wurin haƙar ma’adinai a Jihar Neja.