Wasu ‘yan-ta-kife sun bi dare sun banka wa ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) wuta a Jihar Enugu.
Dandazon ‘yan-ta-kifen dai sun isa ofishin INEC da ke Ƙaramar Hukumar Igbo-Eze ta Arewa wajen ƙarfe 11:48 na dare a ranar Lahadi, inda su ka ci ƙarfin jami’an tsaron ofishin, su ka banka masa wuta.
Kakakin Yaɗa Labaran INEC Festus Okoye ya ce Kwamishinan Zaɓen Tarayya na Enugu, Emeka Ononamadu ne ya sanar da rahoton lamarin da ya faru.
Ya ce daga ciki asarar da ka ɗibga, an ƙone akwatinan zaɓe 748, rumfar zaɓe 240 da kuma kayan ofis, irin su kujeru da tebura.
Ya ce jami’an INEC na ci gaba da duba lafiyar Na’urorin Rajistar Zaɓe, Katin Shaidar Rajista waɗanda ke ajiye cikin wani wurin da wuta ba ta iya lalatawa.
Ya ce tuni aka sanar wa jami’an ‘yan sanda, bayan Jami’an Kashe Gobara sun yi na su ƙoƙarin kashe wutar.
Lamarin ya faru ne a ranar da PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa INEC ta nuna damuwa kan matsalar tsaro da kuma yawaitar sayen ƙuri’u a zaɓen gwamnan Jihar Osun da za a yi ranar 15 Ga Yuli.
A cikin labarin, Shugaban INEC Mahmood Yakubu ya ce matsalar tsaro da guguwar sayen ƙuri’u ne abin da ya fi damun INEC.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce babban abin da ya fi damun hukumar a zaɓen gwamnan Jihar Osun shi ne matsalar tsaro da kuma yadda ake cinikin ƙuri’u ƙiri-ƙiri a fili.
Da ya ke bayani dangane da irin kintsawar da INEC ta yi wa zaɓen, Shugaban INEC Mahmood Yakubu ya ce ana nan ana gagarimin shiri domin tabbatar da cewa an yi zaɓe ba tare da wata tangarɗa ba.
Zaɓen wanda za a yi a ranar 16 Ga Yuli, zaɓen gwamna ne wanda ba ya cikin zaɓen gwamnonin da za a yi na 2023.
Yakubu ya ce ya na kyautata cewa zaɓen mai zuwa zai fi na Jihar Ekiti da aka yi cikin Yuni samun nasara.
Sai dai kuma Yakubu ya nuna damuwa kan matsalar tsaro da kuma sayen ƙuri’u, manyan matsaloli biyu da ya ce su na kawo wa zaɓuka cikas a Najeriya.
“Idan aka dubi abin da ya faru a zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da aka yi baya-bayan nan, INEC na sa-ido sosai kan matsalar tsaro a Jihar Osun.
“Duk da cewa dai a yanzu babu wata barazana, duk da haka mun damu da rahotannin samun ɓarkewar giringimu a wasu yankuna. An hargitsa wurin karɓar karin rajistar zaɓe a Erin Oke da Erin Ijesha. Dukkan su mazaɓu ne a cikin Ƙaramar Hukumar Oriade. Wannan yamutsi har ya janyo ɓacewar karin shaidar rajistar zaɓe guda 46.
“Haka nan kuma ganin irin yadda aka samu yawaitar cinikin ƙuri’u a zaɓukan baya-bayan nan, sayen ƙuri’u na daga cikin babban abin da ke damun mu. Mun gode da irin rawar da Hukumar EFCC ta taka wajen damƙe wasu masu sayen ƙuri’a, waɗanda ke zubar wa dimokraɗiyya da mutuncin ta.”
Ya ce yanzu haka INEC na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da EFCC, domin tabbatar da cewa an gurfanar, tare da hukunta waɗanda aka kama su na sayen ƙuri’u za zaɓen gwamnan Ekiti da aka yi kwanan baya.
Discussion about this post