• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Za a sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya cikin kwanaki uku masu zuwa a jihohi 18 a Najeriya – NiMet

    RANAR ‘YANCI: ‘Yan Najeriya mazauna Landan sun nemi a yi wa gwamnatin NNPP a Kano adalci

    JAllI-JOGAR BELIN DIEZANI A KOTUN LANDAN: Kotu ta hana Diezani fita yawon dare, da rana ma an ce ta maƙala na’urar gane duk lungun da ta shiga

    Ƴan sanda sun damke wasu abokai ƴan kungiyar matsafa dake tsafi da kawunan mutane a Ilori

    Yadda ƴan sanda suka kama Ibrahim da ya yi garkuwa da Fatima, ya ƙarɓi kuɗi kuma ya yashe ta a Zariya

    Kotu ta kori gwamna Sule na Nasarawa, ta ce PDP ce ta yi nasara a zaɓen gwamna

    Ku fito ku ceci mutanen jihar Kaduna kamar yadda kuka yi a zaben majalisun Tarayya da na sanatoci – Isah Ashiru

    An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru

    SSS

    TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa

    Muna ƙarancin malamai, a janye dokar hana ɗaukar sabbin malamai da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba – Jami’ar ABU

    TONON ASIRI: An kama wani Dagaci cikin gungun mahara a lokacin batakashi da ‘Yan sanda

    ‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

No Result
View All Result

KWANAKI 100 BAYAN HARIN JIRGIN ƘASAN ABUJA: Yadda Boko Haram su ka ruguza Kurkukun Abuja, su ka ƙwaci dakarun su 64 da ke tsare

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
July 7, 2022
in Labarai
0
KWANAKI 100 BAYAN HARIN JIRGIN ƘASAN ABUJA: Yadda Boko Haram su ka ruguza Kurkukun Abuja, su ka ƙwaci dakarun su 64 da ke tsare

Bayanan da ke ci gaba da fitowa bayan mummunan harin da ɓangaren ISWAP na Boko Haram su ka kai wa Kurkukun Kuje, har su ka kuɓutar da zaratan su 64 na nuna cewa tsarin tsaro da leƙen asirin Najeriya na da gagarimar matsala sosai.

Kwana ɗaya bayan kai harin, Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyarar gani da ido a kurkukun, inda bayan an kewaya da shi ya ga irin ɓarnar da aka yi, ya cika da mamakin da har ya taƙarƙare a cikin fushi ya yi wa hukumomin tsaron Najeriya tambayoyi guda bakwai da za a shimfiɗa su a cikin rubutun nan.

Boko Haram sun kai wa Kurkukun Kuje hari wajen ƙarfe 10 na dare a ranar Talata. Sun yi nasarar biyan bukatun su da su ka shafe kwanaki 100 su na neman Gwamantin Tarayya ta biya masu, amma abin ya faskara.

Bayan da ISWAP su ka kai wa jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna hari a ranar Litinin, 28 Ga Maris, sun yi garkuwa da mutane fiye da 60, wato adadin zaratan mayaƙan su 64 da ke tsare a Kurkukun Kuje.

Daga cikin abin da su ka buƙata kafin su saki waɗanda su ka yi garkuwa da su, akwai ‘ya’yan su ƙanana da su ka ce an ƙwace daga iyayen yaran mata, aka kai su Jihar Adamawa gidan rainon yara aka tsare.

Bayan an shafe kwanaki ana sa-toka-sa-katsi, an sakar masu ‘ya’yan su, su kuma suka saki mutum 11 daga cikin waɗanda ke hannun su tun lokacin da suka kai wa jirgin ƙasa hari.

Yayin da ake ci gaba da tattaunawa da su ta hanyar ganin an biya masu buƙatar su ta biyu, wadda sauran ‘yan Najeriya ba su san ko wace ce ba, katsam kwanaki 100 cif bayan farmakin jirgin ƙasa, sai ISWAP su ka darkaki Kurkukun Abuja, su ka keta matakan tsaro da ƙarfin tsiya, su ka ruguza kurkukun, har su ka kuɓutar da zaratan su 64, kuma sauran fursunoni fiye da 400 su ka arce, har yau babu labarin su.

Kwana ɗaya bayan kai harin, muhimman batutuwa uku sun faru a ƙasar nan dangane da kai harin. Na farko dai ISWAP sun fito sun ɗauki alhakin kai harin.

Saboda gadara da nuna gazawar jami’an tsaron Najeriya, har bidiyo ISWAP su ka yaɗa, wanda su ka yi rikodin ɗin yadda su ka kuɓutar da zaratan na su, har su na fita su na kabbara, “Allahu Akbar!”

Batu na biyu kuma shi ne bayanin da mai shiga tsakani kuma ɗan sasanta neman mafita, Tukur Mamu ya fitar a ranar Laraba, inda ya sa ya tsegunta wa jami’an tsaron Najeriya yiwuwar kai harin, amma ba su hanzarta yin abin da ya dace su yi ba.

Mamu, wanda shi ne Kakakin Yaɗa Labaran Sheikh Ahmad Gumi, kuma Mawallafin jaridar Desert Herald, ya yi iƙirarin cewa buƙatar ISWAP ta biyu kafin su saki sauran fasinjojin jirgin da ke hannun su, ita ce sakar masu zaratan su 64 da ke tsare a Kurkukun Kuje.

Mamu ya ce an yi ya yin ja-in-ja tsakanin ISWAP da Gwamnatin Najeriya har dai aka sakar masu zarata 10 daga cikin 64.

Ba zato ba tsammani sai aka tashi da rugugin kai hari a kurkukun Kuje, har aka kuɓutar da Boko Haram/ISWAP 64 waɗanda ake ta haƙilon a saki kafin ISWAP su saki matafiyan da ke hannun su.

Gigitar Kuɓutar Da Boko Haram 64 A Kurkuku: Tambayoyi 7 Da Buhari Ya Yi Wa Hukumomin Tsaro:

Bayan ya kewaya ya ga irin ɓarnar da aka yi, Buhari ya yi tambayoyi kamar haƙa:

1. Ta yaya dakarun tsaro su ka kasa hana mahara kutsawa cikin kurkukun?

2. Mutum nawa ne ake tsare da su a cikin kurkukun?

3. Jami’an tsaro nawa ne a bakin aiki lokacin da aka kai harin?

4. Bursunoni nawa su ka rage a cikin kurkukun?

5. Shin ko akwai masu gadi saman hasumiyar-hangen-mugaye daga nesa (watchtower)?

6. Idan akwai dakarun tsaro a kan hasumiyar, me su ka yi to?

7. Shin kyamarar fallasa mugaye (CCTV) ta na aiki kuwa?

Daga nan ne Buhari ya ce gaba ɗayan tsarin leƙen asirin Najeriya ya ba shi kunya, sun zama abin tir da assha.

Lalube A Duhu: An Ɗora Wa Sarakunan Yankin Kuje Alhakin Neman Ɗaurarrun Da Su Ka Arce:

Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja Muhammad Bello, ya umarci sarakunan gargajiya na yankin Kuje su tashi haiƙan su zaƙulo kuma su fallasa duk wani wanda ya ɓoye a cikin yankin, bayan arce daga Kurkukun Kuje.

Ministan ya yi wannan umarni ne a ranar Laraba, lokacin da ya ke ganawa da Sarkin Kuje, wato Gomo na Kuje, Haruna Jibrin.

Bello ya shaida masa cewa akwai buƙatar gaggawa ga basaraken ya sanar wa sauran sarakunan gargajiyar da ke masarautar sa cewa, su haɗa kai da jami’an tsaro ta hanyar ba su bayanan sirrin duk wani baƙon-ido ko mugun da ba amince da shi ba.

Ya ce sarakunan gargajiya sun san duk wani baƙon da ya shiga cikin al’umma ya nemi ya saje da su, ko kuma ya ɓoye a cikin su.

Da Rokoki Aka Fasa Kurkukun Kuje -Wasu Ɗaurarru:

Wata murya da aka yaɗa mai nuna cewa intabiyu ce ake yi da wasu mutum biyu a cikin kurkukun, sun yi bayanin yadda aka ruguza gidan.

Mutanen biyu sun riƙa shaida wa wata mace ‘yar jarida irin yadda ake rugugin harbi a cikin gidan.

Sun shaida mata cewa da rokoki ake harbi a kurkukun. Sannan sun bayyana cewa su ma wata ‘yar kafa su ke son samu su gudu, don kada harbi ya same su.

Wannan lamari dai ya faru a ranar da mahara su ka kai wa tawagar hadimai da masu yaɗa labaran Shugaba Buhari hari a kusa da garin Dutsinma, a Jihar Katsina.

Kuma a ranar ce ‘yan bindiga su ka bindige Kwamandan ‘Yan Sandan Yankin Dutsinma ɗin, wanda ke da muƙamin Mataimakin Kwamishina.

Kurkukun Abuja Da Ke Kuje:

A wannan kurkuku ne ake tsare duk wani babba ko ƙaramin ɓarawon gwamnati, kama daga ‘yan siyasa zuwa manyan ma’aikatan gwamnatin da aka ɗaure kan zamba da satar kuɗaɗe.

A nan ne ake tsare manyan masu laifuka a cikin al’umma da aka yi wa shari’a ko ake kan yi a Abuja.

Tun daga lokacin da aka kafa EFCC zuwa yau, a kurkukun Kuje ne ake tsare gwamnonin da aka riƙa tuhuma da laifin satar kuɗi, waɗanda ake tuhuma Abuja.

Daidai lokacin da aka kai hari a kurkukun Kuje, akwai mashahuran mutane da dama a cikin kurkukun, kamar su tsoffin gwamnoni Joshua Dariye da Jolly Nyame. Kuma akwai Abba Kyari duk a ciki.

Tags: AbujaKujeLabaraiNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

BOKO HARAM A ABUJA: Yadda ISWAP su ka raba wa ɗaurarrun da suka kuɓutar daga Kurkukun Kuje Naira 2,000 kowa ya yi kuɗin mota zuwa gida

Next Post

Idan Uba Sani ya zama gwamnan Kaduna, Daga Mohammed Ibn Mohammed

Ashafa Murnai

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • NASIHA: Ya Allah, Kayi Muna Tsari Da Girman Kai, Daga Imam Murtadha Gusau
  • CUTAR DIPHTHERIA: An samu ƙarin mutum 8,406 da suka kamu da cutar a jihohi 19 a Najeriya – NCDC
  • Za a sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya cikin kwanaki uku masu zuwa a jihohi 18 a Najeriya – NiMet
  • Yadda Ƴan bindiga suka kashe mutum 9 a Avi Kwall, jihar Filato
  • Yadda abokai kuma ɗaliban jami’ar Dutsin Ma, suka kashe abokin su saboda budurwa

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.