Babbar Kotun Tarayya da ke Maimata, Abuja ta tura tsohon Akanta Janar Ahmed Idris kurkuku.
An tura shi Kurkukun Kuje a ranar Juma’a, bayan da EFCC ta gurfanar da shi domin gabatar da ƙarar tuhumar da ake yi masa ta karkatar da Naira biliyan 109.
EFCC ta gurfanar da Idris da wasu mutum uku, waɗanda su ka haɗa da Godfrey Olusegun, Mohammed Usman da kuma kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Ltd.
Sun shaida wa Mai Shari’a OA Adeyemi cewa ba su saci ko sisi ba. Amma dai ya ce a kai su kurkuku a kulle su tukunna. Haka Lauyan EFCC Rotimi Jacobs ya nemi kotu ta yi, kafin ya sake tsara masu wasu tuhume-tuhume a ƙarƙashin Dokar Aikata Manyan Laifukan Zamba ta 109 a cikin Dokokin Najeriya.
Lauyan Idris mai suna Chris Uche ya nemi a bayar da belin su, tunda a baya EFCC ta bayar da belin Idris, amma mai Shari’a ya ce kotu ba wurin wasa ba ce, ana magana ne akan haƙƙin jama’a da ya rataya a wuyan waɗanda ake tuhuma.
An ɗage zaman sai ranar 27 Ga Yuli.
Farkon watan Yuni ne EFCC ta EFCC bada belin Akanta Janar ɗin da ta ce ya kantara satar naira biliyan 84.
Hukumar EFCC ta saki dakataccen Akanta Janar Ahmed Idris, wanda ta kama makonni uku da su ka wuce, bayan ta zarge shi da kantara satar naira biliyan 80.
Kakakin Yaɗa Labaran EFCC Wilson Awujeran ne ya tabbatar wa wakilin mu da sakin da hukumar ta yi wa Idris, a wani saƙon tes da yi masa.
“E, tabbas mun bada belin sa.” Saƙon da ya turo wa wakilin mu kenan a taƙaice.
Sai dai kuma bai sanar da wakilin mu irin sharuɗɗan belin da aka gindaya wa Akanta Janar ɗin ba, wanda a yanzu a dakace ya ke, an ma hana shi zuwa ofis.
EFCC ta kama Idris ranar 16 Ga Mayu a Kano, bayan an sha aika masa wasiƙar gayyata ya ƙi zuwa ofishin ya yi bayanin salwantar naira biliyan 80.
Majiyoyin mu sun tabbatar da cewa EFCC ta daɗe ta na binciken kuɗaɗen, waɗanda ta ce an karkatar da sama da naira biliyan 80 ta hanyar kwangilolin ƙarya.
Kamfanonin da aka riƙa damfara wa kuɗaɗen duk iyalan sa ne da makusantan shi Akanta Janar Ahmed Idris ɗin ne. Haka dai wani mai bincike ya tabbatar.
Tuni dai aka dakatar da Ahmed Idris, sannan aka hana shi duk wata mu’amala da ma’aikatan ofishin sa.
Discussion about this post