To ance dai, karshen tika tik, kowa ma dai yau a Nijeriya a ko ina yake, kuma ko menen matsayin sa, ya san cewe wankin hula yana neman kaiwa Shugab Buhari dare.
Kafin kasancewar Buhari ya zama shugaban kasa ya kasance mutum ne mai radin kare hakin Dan Nijeriya kuma ba ya yin hakuri wajen nuna bacin ransa a baya, duk lokacin da aka ga gazawar gwamnato cin baya, walau a harkar tsaro, wutar lantarki, ilimi ko kuma kiwon lafiya.
Wai shin yau me ke faruwa ne da Shugaba Buhari? Yana kallo a hankali Nijeriya tana narkewa, a yau fa harkokin ilimi a Nijeriya yana cikin tasku, yau ba a karatu a jami’oin Nijeriya, kazalika harkar lafiya, wutar lantarki duka suna cikin kalubale matsananci.
Kuje da Abuja, tasku ne babba, barin yan ta’adda su samu gindin zama a Jihar Kaduna da Jihar Niger, tamkar wani shiryayyan abu ne, na kawo karshen Abuja. Ba karamin sakaci a ka yi ba na barin kungiyoyin ta’addanci irin su ISWAF a ce suna da sansani a Kaduna da Niger ba, duk da kasancewar masana da dama da ma hukumomi sun ankarar da gwamniatin a kan wadannan yan ta’adda tun kafin suyi karfi kamar haka.
Wai shin ina ministocin Buhari na tsaro da shugabbanin tsaro dama na legen asiri da ya aminta da su, suke aiki tare? Wai shin ina yawan kudaden yan Nijeriya da ake narkawa a kan harkar tsaro nan ne?
Anya kuwa lokaci bai yi ba da Shugaba Buhari zai yi nazari a kan makusantan ba, musamman wanda ya dankawa amanar tayi shi mulkin Nijeriya ba, wai ina ministo cin sa?
Yaufa tsabar tabarbarewar tsaro, kowa yaga abun da ya faru, na fasa Gidan YArin Abuja da ke Kuje da ke, a bude da tafiya da manyan masu laifi ba tare da wani katabus na jami’an tsaro ba, abin takaici ance dukanin yan Boko Haram din da a ke tsare da su, sun fece, banda sauran masu manyan laifi wanda suma aka kubutar da su.
Babban abin tahin hankalin ma kuwa shine, wai wannan aika-aikar a cikin garin Abuja, Fadar Shugaban Kasa aka yi ta. Wai shin a irin wannan jagorancin shi kansa shugaban kasa yana da tabbas din kyakkywan tsaro kuwa?
Abin tashin hankalin shine rahotannin da suke fitowa cewa, a kwai rahotanni da suke nunawa cewa an tsiritawa hukumomin tsaro yiwuwar kaiwa wannan harin, amma duk da haka sai da maharan suka yi nasara.
Kaito, babban abin da ya bawa kowa mamaki shine, fadin Shugaba Buhari na cewa hukumomin san a bayanan sirri sun bashi kunya, to in har hakan gaskiya ne kuma ya ratsa zuciyar sa tabbas lokaci yayi a wurin sa da ya kamata yayi duba na tsinaki a cikin makutan sa, musamman wayanda ya aminta da su wajen gudanar da gwamnatinsa.
Dutsinman Katsina, a can ma jahar da Shugaba Buhari ya fito, sun fi kowa shiga masifar mummnan tukin wanna gwamnati na samar da tsaro, ana cikin alhinin bindige jami’in dansada mai matsayin Assistan Commissioner, kuma jami’I mai kula da yankin Dutsinman, sai gashi Ýan Bindigar Daji sun yi wa tawagar Shugaba Buhari kofar rago a kan hanyar su ta zuwa Daura garinsu Buharin.
Irin wanan cin fuska da me yayi kama. Wai shin wannan ba alamu bane na gazawar dukkanin dabarun da wanan gwamnati take yi ba a harkar tsaro.
Tabbas, lokaci yayi da Shugaba Buhari ya kamata yayi nazari a kan duk wayan da ya yarda da su kuma ya ke aiki da su a gwamnatin sa, domin cigaban Nijeriya nasarar sa ce kuma akasin haka gazawar sa ce.
Babu yadda za’ayi Shugaba irin na kasa kamar Nijeriya wanda tafi kowace kasa a Africa bunkasar tattalin arziki kuma tafi kowace kasa karfin tsaro a nahiyar Africa, irin wadanna shedana suna faruwa haka siddan ba tare yin haffasa ba na kawo chanji ba.
Babu yadda za’ayi Shugaba ya zauna da yan majalissar zartarwar sa (Ministoci) sama da shekara bakwai ba tare da sun taimake shi ya kawo chanji ba kuma kullun yana karbar uzirin su a kan suna kokari ba. Wai shin yaushe kokarin nasu zai haifar da ‘da mai ido ne?
Sun kasa shawo kan matsalar ilimi, sun ma kara matsalar fiye da ta badi, sun kasa shawo kan matsalar wutar lantarki, tama karu fiye da ta badi. Sun kasa kawo matsalar tsaro, kiyasi ya nuna kullum yan Nijeriyar da basu jiba basu gani ba kimanin mutun talatin suke rasa rayukan su a duk tsawo rana, a yau muna daga cikin jerin kasashen da mukafi kowa rashin tsaro a duniya, duka da kasancewar kasar mu ce tafi kowa karfin soja a Nahiyar Africa.
Kodai Shugaba Buhari ya farka, yayi dogon nazari a kan makiyan sa na kusa ko kuma na kusa da shi wanda basu da wata hikima da basira da za su iya taimakon sa wajen mulkin Nijeriya ko kuma gwamnatin ta kare a irin wannan yanayi. Shekaru bakwai ba kwana bakwai bane, in har dabaru da ake gwadawa a shekara bakwai basu yi magani ba to fa ya kamata a sake wani tunanin.
Tabbas Shugaba Buhari a wanna lokacin da ya rage masa yana iya kawo chanjin da zai taimakeshi sauke amanar da ke kansa a kan yan Nijeriya, in kuwa ba haka ba wankin hula zai iya kaishi dare, yayi zuwan kare karofi banu rini babu tatsa.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post