Mai barci ya tashi, na tsaye ya zauna, mai tafiya ya dakata ya sha labarin yadda tsohon ɗan Boko Haram ya zama ma’aikacin tsaro a gidan kurkuku, wanda aiki ne gwamnatin tarayya ke ɗauka.
Ranar 18 Ga Fabrairun da ya wuce ne balli ya tashi a Sabon Gidan Kurkukun Yola a Jihar Adamawa, inda aka gano cewa a cikin sabbin ma’aikatan kurkukun, har da wani gwanin iya harbi da sarrafa manyan bindigogi mai suna Wilberforce Yohanna.
Hankalin manyan jami’an kurkukun ya tashi da su ka gano cewa Yohanna tsohon ɗan Boko Haram ne.
Wasu sahihan bayanan sirri da Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta rubuta dangane da Yohanna, sun faɗo hannun PREMIUM TIMES, wadda bayan ta tabbatar da lamarin, buga labarin ya zama wajibi.
Yadda Aka Gano Yohanna Tsohon Ɗan Boko Haram Ne:
An gano Yohanna tsohon ɗan Boko Haram ne tun a wurin bada horo ga sabbin-yanka-raken da ake ɗauka, inda aka je koya masu yadda ake sarrafa bindiga ƙarama da babba.
Jami’an bayar da horo sun lura ko a cikin su babu wanda ya kai Yohanna iya sarrafa bindiga ƙarama ko babba. Iya loda harsasai da hanzari a cikin ƙwarewa, ba a fi shi iyawa ba, sai dai ya koyar, amma ba a koya masa ba.
Yohanna ya zama abin kallo ga jami’an bayar da horo ganin yadda ya ke yi wa bindiga filla-filla, ya kuma haɗa ta a cikin ƙwarewa. Tun a wajen riƙe bindiga babba da ƙarama aka fahimci Yohanna da wani gogarma ne.
An tafi da shi wajen masu bincike, inda bayan an sheƙa masa ruwan tambayoyi, sai ya faɗa masu cewa a gaskiya shi fa tsohon ɗan Boko Haram ne.
Yohanna ya shaida masu cewa amma shi ba aƙidar Boko Haram ya ke da ita ba. Ya yi iƙirarin cewa kama shi ‘yan Boko Haram su ka yi, su ka kuma tilasta shi ɗaukar makami ya taya su yaƙin tsawon shekaru biyu. Daga baya ne ya ya samu wata dama da sa’a, ya tsere, ya kuɓuta daga hannun su. A cewar sa fa.
Sai dai kuma ba a tantance ba shin bayanin yadda ya shiga Boko Haram ɗin da ya yi gaskiya ne, ko kuma ya danne gaskiyar, ƙarya kawai ya yi?
An ɗauki Yonanna aikin kula da kurkuku watanni biyar kafin Boko Haram su kai wa Kurkukun Kuje mummunan harin da har su ka kuɓutar da ‘yan uwan su 64 da kuma haddasa arcewar ɗaurarru fiye da 400.
Majiya daga kurkukun ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa lamarin Yohanna ya zame wa Hukumar Kula da Kurkukun Najeriya alaƙaƙai. Ga shi dai an samu tantagaryar ɗan Boko Haram a cikin su, amma ba a son ɗaga murya don kada ‘yan jarida su yi labari su watsa duniya.
Binciken da PREMIUM TIMES ta yi a cikin jami’an da su ka nemi a ɓoye sunan su, sun tabbatar da cewa, irin birkitaccen tsarin da ake bi idan za a ɗauki sabbin jami’an kurkuku, lalataccen tsari ne, wanda kuɗi kawai mai neman aiki zai biya a ɗauke shi aikin.
“Ba a maganar cancanta, kawai iyar kuɗin ka iyar shagalin ka. Wanda za a ɗauka a matakin Level 8 na ma’aikacin gwamnatin tarayya, zai biya naira 800,000. Matakai na zuwa na ƙasa kuwa a kan biya naira 400,000 ko sama da haka.” Inji wata majiya da ta ce shi ya sa mai laifi ba zai yi wahalar samun shiga aikin jami’an tsaron kurkuku a Najeriya ba.
Idan ba a manta ba, tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Sanata Ibrahim Geidam ne ya bijiro da ƙudirin yafe wa tubabbun Boko Haram, a Majalisar Dattawa, kuma aka amince har ƙudirin ya zama doka cikin 2020.
Bayan ƙudirin ya zama doka, an kafa Hukumar Yi Wa Tubabbun Boko Haram Wankin Kankarar Mummunar Aƙida, Koya Masu Sana’o’i da Maida Su Cikin Jama’a.
Sai dai kuma mutane da dama sun riƙa kushe wannan shiri, su na cewa wasu ba tuba su ke yi ba, su na komawa daji wurin Boko Haram duk su kwashi bayanan sirri su kai wa kwamandojin Boko Haram.
Yayin da al’ummar da tubabbun ‘yan Boko Haram ɗin su ka fito cikin su ke ƙyamar sake zama tare da su, Gwamna Babagana Zulum na Barno ya taɓa cewa shirin tarairayar tubabbun ‘yan Boko Haram ɗin ba shi da fa’ida, domin wasun su daji su ke komawa su sake ɗaukar makami.
Sannan kuma za a iya tunawa a ranar Alhamis ce Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya yi iƙirarin cewa shi ya na ganin da haɗin bakin wasu jami’an kurkuku Boko Haram su ka fasa kurkukun Kuje.
PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran Hukumar Kula da Kurkukun Najeriya, Abubakar Umar, wanda ya ce labarin ɗaukar tsohon ɗan Boko Haram aikin tsaron kurkuku ba gaskiya ba ne, ƙarya ce.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa shi ma ɗin bai faɗi gaskiya ba, domin labarin ɗaukar Yohanna aiki ya bazu sosai a cikin manya da ƙananan jami’an Hukumar Kula da Gidajen Kurkukun Najeriya.
Discussion about this post